Menene Maganin Rashin Sha'awa Ga Mace Mai Aure?

Menene Maganin Rashin Sha'awa Ga Mace Mai Aure

Menene Maganin Rashin Sha'awa Ga Mace Mai Aure 


Tambaya 


Malam Dan Allah menene magnin rashin sha'awa ga macen aure kuma menene yake kawota Allah yakarawa malam lafiya da ilimi mai amfani


Amsa 


Toh dai ita sha'awa bata da tasiri ga wanda yake da damuwa ko Rashin kwanciyar hankali da Kuma rashin jin dadin zaman da miji. Sannan Kuma akwai Wanda halittarsu Haka Allah ya haliccesu basu da karfin sha'awa domin akwai bambancin sha'awa kafin aure da Kuma sha'awa bayan aure anan ake banbance mai karfin sha'awa da mai saukin sha'awa domin zakiga wani kafin aure Kamar zai ci babu amma ana gama cin amarci sai kiga sha'awa tayi lakwas. Wani Kuma sannan Zaki ga Sabuwar sha'awa ta bayyana gareshi shiyasa ba'a hukunci da sha'awa sai mutum yayi aure Kuma anga yadda sha'awarsa ta kasance.


Maganin Rashin Sha'awa 


Sannan ga Mata amare bazasu iya tantance sha'awasu da gamsuwar aure ba sai sun dan Jima a gidan miji domin na farko Jin zafi da fargabar saduwa na hanasu Sha'awa, ni'ima da kuma gamsuwa akan hakane ma Zaki ga mace na jin sha'awa amma mijinta na zuwa kanta sai sha'awa ta dauke ta nemeta ta rasa sabida ba yadda za'ayi a samu biyan bukata mutukar ba nutsuwa, shauki da karkashi a wajen ibada aure. 


Sanan Kuma ciwon sanyi na taka rawa wajen dakushe sha'awa da gamsuwa.


Haka kuma kiyayya ga miji ko Jin haushinsa daliin wani Abu da yayi mace ya taba Mata zuciya duk suna hana sha'awa tasiri. 


Ita fa sadurwa auren bata da tasiri mutukar tsakanin mata da miji basu samu karsashi ba da son abin a lokacin da zai faru Amma mutukar wani bashi da annashuwa to dadin zai zama ragagge sai dai ayi dan biyan bukata amma ba dandana zakin Jima'i ba. 


Maganin Rashin Sha'awa


Amma ga dan wani hadi da zai iya taimakawa wajen motsa sha'awa ga mace ko namiji amma shima ba zai tasiri ba matukar da abinda na bayyana a sama.


A samu wadannan abubuwan kamar haka: yansun, 

  • garin ruman, 
  • cittta, 
  • kanimfari 
  • Na'a na'a 

ko wanne cokkali daya sai a dakesu su Zama gari sai ki samu zuma mai kyau mara hadi, sai ki zuba a ciki ki dafa kamar minti 10 a garwashi Amma kada ya kone, Zaki dinga Sha Babban cokali 1 safe da yamma sati 2 zakiyi, ko Kuma a dinga dibar teaspoon asa a kofi sai a zuba tafasasshen ruwan zafi a kansa a bashi mint 15 sai asa Zuma cokali 1 Asha sau 2 a rana. Insha Allah wanan zai sa sha'awa da samun nutsawa da sa annashuwa ga ma'aurata yayin ibadar aure. 


Allah ta'ala yasa mudace 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post