Menene Maganin Rage Sha'awa? |
Likita shin baku da maganin rage sha'awa ne, ina daf da afkawa zina, karfin sha'awa ta yai yawa
AƘallah cikin sati guda na sami makamantan wadannan tambayoyin guda takwas, Wanda tambayoyi 6 sun fito ne daga Maza, 2 kuma daga Mata. Amma idan tattara adadin irinsu zan daga farkon shekara zuwa yau toh wallahi nima bansan adadinsu ba irin wadannan tambayoyin.
Ko shakka babu duk wanda ya doso ka da irin wannan tambayar toh alamace ta mutum yana da tsoron Allah. Yana matukar tsoron Allah, yana kuma tsoron saɓamasa, domin wanda ke bin son zuciya ba zai ma taɓa tunanin neman shawara ko mafita ba, abunda kurum zuciyarsa ta basa shi yake yi.
Shyasa yau Matasa da yawa sun kashe gobensu batare da sun san hakan ba, yayin da suka shagala zagin gazawar shugabannin, sun mance Zina da Talauci tamkar Hanta da Jini ne, basa rabuwa, inde akwai yin kudi a agenda dinka kuma kake aikata zina toh ka dena yaudarar kanka gaskiya. Idan ko kaga me kudi na zina toh ka tausaya masa domin tabbas babu kokonto Arzikinsa na lahira yake cinyewa tun anan don haka sune ubangiji ya kirasu da AL-ASHQA talakawan lahira, zasu shiga wuta ma'abociyar zafi.
Sannan a irin haka wasu illarsu ma sai sun duba Mata masu mutunci, masu addini, sun nuna musu so, kuma Matan sun ďau soyayya sun basu, har tayi tasiri a zukatan sisters din. sannan kaga sun fara shigo musu da zantuka na banza, wai su irin wannan nagartattun suke son ɓatawa koma su ɓata, "subahanalla! Wanda wannan cin amana ne, hakan na nuna babu wanda ya tsira. Bana taba zargin Mace budurwa da lalacewa sai dai ko matar aure ba, amma yan Mata Mazan ne de ke batasu.
Domin mu ba ma'asumai bane, komi addinin Mace wani namiji nada tasirin iya warware tarbiyyarta ta shekara 25 cikin minti 5 wallahi, musamman inta bashi yadda bata ta6a zaton cutarwa daga garesa.
Toh Allah ka cigaba da tsare yan uwanmu damu kanmu daga sharrin sha'awa tare da masu biyemata amin
Sannan Yin Wasa da al'aura ba Mafita Bane(maganin rage sha'awa)
Kwarai kuwa wasa da al'aura (Masturbation) nada tarin illoli, Amma in a likitance za kai ta bin Internet ba zasu faɗama illar ba sai de ma a nuna kamar Baida illah, domin sai anyi analysis ake iya bada bayani kan abu wanda har yau tattara matsalolin ake.
Amma dai daga complaints din irin wadanda suka rika yi wanda yau suke haduwa da matsala akwai tarin illoli, kai yana iya kai mutum ga ciwon kwakwalwa ma.
Duk mai wannan aiki zai iya gamuwa da wadannan larurori kamar haka:
- Larurar yawan mantuwa gami da shiririta ta yadda duk karatun da mutum yake ganewa zai dawo ya daina fahimta, ko yayi baya zama.
- Kankancewar gaba zuwa karami ko azzakarinsa ya tattare ya rika komawa ciki.
- Zai Haddasa wa mutum saurin inzali, ya rika saurin kawowa yayin jima'i, kai wani ko minti daya baya iya yi yayin tarawa da iyalinsa, Kai wani kafin Ma ya kai ga macen sai yaji ya kawo kuma ba zai iya komawa ba.
- Rashin karfin mazakuta har ta kai gabansa bama ya iya tashi koda ya tashi sai dai ya koma ya kwanta sai ya ita girgije-girgije, bazai iya gamsar da iyalinsa ba, wanda hakan na iya komi son da Mace kema ta nemi saki.
- 'Karancin sha'awa bayan aure, kai ko film din batsa da kake kallo zaka ji abunda ada yake kayatar da kai a hankali inma ka kalla baka jin yadda kake so. Toh haka a hankali mutum zai rasa sha'awarsa.
- Matsalar karancin maniyyi wanda hakan nada illoli da yawa, kamar haifar da rashin iya yiwa Mace ciki ballantana iya haihuwa da dai sauransu.
- Cutar damuwa, tare da raunin jiki, yasa zuciya take birkicewa mutum yaji tana bugawa farfar da sauri, tare da kara munin hawan jini wanda sashin mutum na iya shanye wa musamman me sannan nen hawan jini da baya bashi kulawa.. Yayin MASTURBATION jini na hawa koda kuwa baka da hawan jini.
- Lafiyar gani, inya tsannanta yana iya shafar idon mutum.
-Illolin masturbation nada yawa, kowa da akwai ta inda illar ke farmasa ba wanda yasan ta ina zata fara don haka mutum ya kiyayi kansa kurum.
Ai duk abunda addini ya hana to kiyayarsa shine zaman lafiya domin kasan dole akwai illah kam
Amma ga me da waccan tambayar ta Farko kan maganin rage sha'awa
Dangane da waccan tambayar akoda yaushe bada idon likitanci kurum muke kallon matsala ba, wata matsalar bata bukatar shan kwayoyin magani kurum magana takeso taji na karfafa guiwa daga wanda zuciyar ta nutsu kuma aminta dashi wanda likitoci na ciki, domin matarka na iya boyema damuwa amma idan ta zo gaban likita ba abunda bazata amayar ba saboda waraka take nema.
Amma anan inason tunasar damu irin girman laifin zina, ita ZINA sam bata kashe sha'awa, tana kasheta ne kurum na ɗan wani lokaci wanda daga sanda aka farata to fa mutum ya budewa kansa kofar talauci, kaskanci, kuncin rayuwa, nadama, lalacewar jiki, asara da masifu gakai.
Kai uwa uba ma mahaifanka ko mahaifanki ba irin ɗa ko ƴar da sukai fatan a ce sun haifa ba kenan, sun raineka ne ka zama mutumin kwarai, ko mutuniyar kwarai domin duk abunda kayi koda bayan ransu suna da kamashon aikin dakai kuma zaije musu a kabari.
Duk shari'oin Allah ba wanda ZINA ba ta rusasu, cikakkiyar fitsara ce, cikinta ake samun dukkan wani nau'in sabon Allah, raunin addini, raunin aqidah, rashin kishi, rashin ganin girman manzon Allah, kisan kai, annamimanci, karya, cin amana, tare da bude kofofin talauci da annoba ga hatta wanda baiji ba, bai gani ba.
Duk tsananin sha'awarka akwai wanda suka fika, domin wasu hadda larura kuma hakan baisa sun biye mata sun saɓawa Allah ba. Kai ko mahaukacin dake yawo a bola yana da sha'awa amma bai zina da mahaukaciya yar uwarsa ba ballantana kai mai hankali da tunani.
Muddin ka kuskura ka fara zina tohfa ko kai aure ba baki naiwa mutum ba amma da wuya ya dena, domin maganinta shine kar afara.
- Shawara ta farko anan ga duk wanda ke cikin yanayin wallahi muddin yana da halin aure toh kai tsaye yai AURE koda hakan na nufin tsayawar karatunsa muddin bazai iya riqe kansa ba. Yafi kaje kana jawowa mahaifa da ýan uwa abin kunya tare da karin masifu akan mu sauran al'umma wanda dama a yau gasu muna ciki na kashe-kashe da sace-sace da annoba, duk zina na daga sillar haka.
Don haka tunda mutum gashi ya balaga jikinsa ya nuna yanason auren toh ya nemi tallafin iyayensa inma baida halin yi, ko tallafin yan uwansa ya sanar dasu bukatarsa ta aure afili su tallafa, babu sama dasu.
In kuma ba halin abun auren to ka nemi ataimaka ma da jarin sana'ar yi wacce in Allah ya dubi niyya sai kaga yasa albarka ciki ka sami abun yin auren.
Musulunci addini ne da aka ginashi don a cire barna cikin jama'a akawo musu gyara. Yau da gobe tabbas itace aure, inza'ai dole ya zamto akwai abun iya rike iyalin. Amma de aure misamman ga namiji baya hana karatu sam-sam, saide kurum tunanin karin nauyi, amma in haka ta faru biyun sun taso lokaci guda toh azaɓi mafi mahimmanci abar daya, wanda anan auren yafi mahimmanci.
Ko bangaren iyaye rashin fahimtar addini ne kace yaro ko yarinya sai yayi karatu dole kafin ai masa aure alhalin ya bayyana yana da bukata, idan bai bayyana ba shikenan, tunda da akwai masu iya jurewa har su kammala karatun lami lafiya amma basu da yawa. Don haka da wannan qin karatun ai aure da kuma yaro yaje ya kama zina wanne yafi muni? Zina tafi ILLAH.
Don haka inde shawarace inkana da hali kai Aure, idan babu a taimaka ma da jari ka kama sana'a ko abarka kaje ka nemi aikin a company ko wata ma'aikata ka sami abunda zakai ma kanka aure koda hakan yana nufin barin garinku ne kam.
- Sai karin shawara ta biyu da zan ba irin wadannan shine; su rinqa jaraba yin azumin ranakun litinin da kuma alhamis Insha Allahu hakan zai ragema mutum karfin sha'awar, bazai yiwu ace baya ragewa ba, abunda ke faruwa sanda mutum ya dau azumin yakan jure rike duk sha'awarsa amma da ansha ruwa sai ya saki jikinsa wannan tasa wasu kanga kamar insun sha ruwa sha'awar tafi karuwa, kurum raunana ransu da cewa ai an sauke azumi ke jawo hakan.
Idan kuma sha'awar karfinta yakai ga azumin litinin da alhamis bai rageta ba. To ka rika azumin annabi Daud (AS) wato yau kai zumi gobe kasha ruwa. Yau kai azumi gobe kasha ruwa. Haka dai har Allah ya yaye ma. Insha Allahu zaka sami sassauci musamman in Allah ya dubi niyyarka, ga lada ga kariya.
Domin Manzon Allah (SAW) cewa yayi yaku taron Matasa wanda keda Halin aure yaje yai aure, wanda bashi da iko to ya cigaba da azumi, Annabi yace azumi na rage sha'awa.
- Sai Abu na uku duk damu a likitance bamu da tabbacin ingancin hakan amma dai munsan da akwai Alternative medicine wato traditionally wanda kuma a irin nan mukanji da yawa na nuna idan suka sha lemon tsami ko suka jiqa kanwa suka shaa hakan nasa su sami sassauci. Don haka in mutum ya yanka, ya matse lemon tsamin sai ya qara ruwa yasha, in bai masa ba ya qara yanka wani koh Allah zaisa a sami sassauci.
ALLAH kuma shi yayewa duk sauran al'umma dake fuskantar hakan, domin na tabbata irin wannan larurar ta tsananin sha'awa kwai tarin mutane cikin Maza da Mata masu fama, bakowa bane mazinaci duk da lalacewar zamani.