Menene Ciwon Sanyi? |
Duba da yanayin wannan tambayar tana buƙatar bayani gaskiya, misali: akwai fahimtar da al'umma su ka yiwa ciwon sanyi mu a al'adance, da kuma ma'ana ta ilmin likitancin gargajiya, da na zamani. Kuma duk wannan ma'anar daban daban suke bawa ciwon sanyi kai har su kansu ƴan boko masu cewa infection din idan sun ce infection kawai abu daya suke nufi shine ciwon da ya shafi mata ko al'aura kuma lay man's understanding ne.
Shin Menene Ciwon Sanyi?
A likitance idan aka ce ciwon sanyi abune a zahiri wanda yake da alaƙa da shi kansa sanyi na zahiri wanda yake iya attackin respiratory tract(upper ko lower) kamar su pneumonia, asthma, mura, coryza, da sauransu, kuma ko wanne da irin sings &symptoms din da zai iya zuwa maka dashi. Ko idan mutum yana aiki a guri mai sanyi, ko mai ice, ko masu kamun kifi, etc.
-Mata su kuma ciwon mata da ake alaƙantawa da sanyi mafi yawa ba sanyi bane wani yana samuwane saboda rashin tsafta ta jiki, tupapi, ko toilet,
-Sannan akwai wadda ƙwayar cuta ke sakawa kamar bacteria, virus da fungi. Kamar su pelvic inflamatory diseases, syphlis, gonorrhea, da sauransu. kuma yana iya kama maza da mata so shawara itace idan mutum yaji wata alama kawai yaje gurin likita. Allahu aalam.