Menene Basir Da Abubuwan Dake Kawo Basir?

Menene Basir Da Abubuwan Dake Kawo Basir?
Menene Maganin Basir



Kafin mu yi magana akan maganin Basir yanada muhimmanci mu fara fahimtar ma menene Basir ?


Da farko dai a cikin duburar 'dan Adam akwai jijiyoyin jini wadanda wani lokacin suna samun matsatsi da talala mai takurasu. A lokacinda suka samu takurawa da yawa, sai su kumbura. Wanda Kumburin wadannan jijiyoyin jini da kara matsi da takura a garesu cikin dubura shi ya ke sa wa kaga wani tsiro ya fito maka a bakin dubura wanda jijiyar jini ce.


Za ka ji ciwo, ko kai-kayi, wani lokacin ma har da zubar jini. Wannan shi ake cewa, basir-mai tsiro. Da akwai kuma nau'in Basur mai sanya yawan fitar hutu wato tusa da kuma wanda ke sa cushewar ciki ko yin kashi mai tauri. Wani basir din kuma har yana sa tsatstsagewar dubura yayin fitar bayan gida. 


Menene Alamomin Da Mutum Zai Gane Yana Dauke Da ciwon basur? 


Akwai alamomi na fili da na boye da mutum zai gane a lokacin da ya kamu da cutar basur kamar haka; Mutum zai rika fama da wadannan matsaloli


  • Kaikayi a dubura da bacin rai.
  • Fitar jini idan ana bayan gida amma ba tare da anji zafi ba.
  • Ciwon jiki da rashin sakewa.
  • Kumburar dubura.
  • Fitar kashi curi-curi ko dunkule-dunkule tare da wahala. 


Menene Riga-Kafin Ciwon Basur? 


Wanda yake gudun kamuwa da cutar Basur sai ya yawaita shan dauri da daci, kamar gauta da sassaƙen mangwaro ko sassaƙen ɓaure ko madaci, ko mur da makamantansu. 


Sai dai a kula, kada a matsawa shan daci saboda matsalolin hanta. 


Menene Maganin Basur? 


Idan an riga an kamu da ciwon basur kuma sai a gwada daya daga cikin wadannan hanyoyi domin yin magani:-


Hanya ta farko 

A samu wadannan abubuwan kamar haka ;


  • lemon-tsami guda uku, 
  • tsohuwar-tsamiya guda uku, 
  • jan-gauta guda uku, 
  • barkono guda biyar, 
  • sabulun sha kamar girman lemon tsami.


Idan aka tashi sai a hade su waje daya, a jika su kwana. Kullum sai a zuba rabin kofi a sha da safe kafin a ci abinci. Ana diba ana kara ruwa, har sai ya salamce sannan a zubar.


Wannan magani ne na Basur sosai. Indai ka hada shi zai warke, ka rabu da shi da izinin Allah. 


Hanya ta biyu 

A samu madacin qasa daidai misali, a wanke shi, a zuba a cikin tukunya. A zuba ruwa da jar kanwa kadan, a dora akan wuta.


Idan ya huce, sai a dinga shan rabin kofi kullum sau uku. Da safe rabin kofi, da rana rabin kofi da daddare ma rabin kofi. 


A dinga sha kullum ana kara ruwa har ya salamce. A cigaba da hadawa har sai an warke sarai. 


Hanya ta uku 

A samu wadannan abubuwan kamar haka ;


  • sassaƙen itacen mangwaro,
  • sassaƙen kadanya, 
  • sassaƙen dorawa, 

sassaƙen madaci amma madacin kadan ake bukata.


Sai a hade su waje daya a wanke a zuba jar kanwa kadan. A tafasa, kullum a sha rabin kofi sau uku kafin a ci abinci.


Idan kuma basur din mai tsiro ne ko wanda ake fitar baya, to idan an tashi sai a tafasa magungunan a zuba ruwan a cikin babban mazubi. Sai ka tsuguna, tururin ya dinga shiga karkashinka, idan ya dan huce kuma sai a shiga ciki a zauna tsawon yan mintuna ko kuma a dinga kama ruwa da shi.


Insha Allahu indai an hada wannan ana sha ana shiga ciki, to lokaci kadan za a rabu da basur kowane iri ne. 


Hanya ta huɗu 

A samu ɓawon dorawa, a hada da jar kanwa a tafasa. Sai a dinga tsugunawa yadda tururin zai dinga shiga cikinka sosai, idan ya dan huce sai a shiga ciki a zauna ko a dinga kama ruwa da shi. Sannan a dinga tsiyaya ana sha. Shi ma hanya ce ingantacciya ta maganin basur. 


Hanya ta biyar 

A samu man habbatussauda da man tafarnuwa da man zaitun. Sai a hada su waje daya. Sai ka samu auduga mai kyau ka dangwali wannan man kayi matsi da shi a karkashinka, musamman in za ka kwanta da daddare. Kullum ka dinga yin haka sau daya. Wannan yana saurin kashe basur mai tsiro da maganin tsatstsagewar dubura. 


Hanya ta shida 

A samu garin sanamakiy da zuma. Sai a tafasa garin rabin cokali, a sa zuma daidai gwargwado. Sai a sha kullum sau daya.


Yana maganin kashin jini, da taurin bayan gida, yana fitar da dattin ciki a cikin kankanin lokaci. Sai dai wannan banda mace mai ciki, banda yara kanana. 


Hanya ta bakwai 

A samu ƴaƴan raidore da kumfar maliya da garin bagaruwa, sai a hada su waje daya a tafasa. Sai ya tsuguna tururin ya dinga shiga jikinsa, idan ya dan huce sai ya zauna a ciki ko kuma ya dinga kama ruwa da shi. Wannan yana kone tsuron basur yana maganin tsatstsagewar dubura. Allah ya bamu dacewa.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post