Menene ake nufi da daren farko? |
Mutane da dama musamman wadanda suke shirin yin aure suna yawan tambaya kan, menene daren farko da yadda akeyinsa?
Hakan yasa na kawo muku cikakken bayani kan abinda ake nufi da daren farko da kuma yadda ake yin sa kamar haka.
Daren farko ko kuma daren angwanci, wani dare ne da ake farin ciki tsakanin ma'aurata, idan an wayi gari cikin sa rana ce masoya basa mantawa da ita a matsayin ranar farin ciki.
Menene ake nufi da daren farko?
Ma'aurata za su kasance a wani hali mai tattare da shauki da zumudi na kasancewar su a matsayin abu daya. Daren daraja ga ma’aurata kenan da zarar an kai amarya gidan mijinta ango kenan, Iyayanta da kawayenta za su barta a daki tana jimamin kasancewar ta a wannan yana yi na kasancewa amarya.
Akan so bayan an watse an bar amarya ta tashi ta dan gyara abin da take ganin ba zai kayatar mata da ango ba. A wasu wuraren kawayan amarya suna tsayawa har sai an kawo ango, wannan baya cikin al’ada an fison abar amarya daga ita sai ango su ci amarci kai ango ka shigo kuyi abinda addini Ya yarda dashi Na sanarda ita yaya addini kuyi sallah ku yi godiya ga Allah ku ci daga abinda Allah Ya baka a wannan dare domin more amarci.
Na biyu shine kokarin tafiyar da kunya tsakanin ma’aurata. kasancewa sababbin ma’aurata duk baki suke ga wannan harka ta ibadar aure, dole Ya kasance akwai kunya da yar fargaba game da daren, don samun cikakkiyar nasara daren farko, sai ma’aurata sun rage jin kunyar dake tsakaninsu, Ya kasance suna tattaunawa kan batun ibadar aure, da yadda suke fatan daren farkonsu Ya kasance da kuma dokinsa dasa kyawawan tunani cikin zuciya game da shi tun kafin zuwan ranar a nan aikin ango ne ya rika Bi a hankali, cikin wasa da raha da zolaya ta hanyar amfani da kalmomi makimanta ba masu nauyi ba.
Kuma Ya kasance suna cike da shauki, har yaga ya zakulo amaryarsa ta rage jin kunya, idan ma dai ba ta daina ba, fada matan zai sa ta zama cikin sanin abinda ka iya faruwa, haka kuma yana da kyau ma’aurata su nema tare da karanta littafai dasu kai bayani kan ilimi ibadar aure don a fahimce su.
Daga cikin bayani kan Menene ake nufi da daren farko da yadda ake yinsa, akwai bayani kan SHIRYA JIKI DA JINI: domin dai jiki da jini kamar inji ne ga fetur din gabatar da ibadar aure: don haka yana da muhimmanci ga ma’aurata su inganta lafiyar jikinsu da ta jininsu ta hanyar cin abinci mai kyau da gyara jiki musamman ganyayyaki da ya’yan itatuwa da yawan motsa jiki da sauran shirye -shirye makamanta wadannan yin kyakkyawa zato game da juna: ango Ya sani abubuwa da yawa Na iya ballewa mace murfin budurci ta daga cikinsu akwai;
1. Jinin haila mai nauyi
2. hawa sama, itace, gini da sauran su.
3. tsalle-tsalle, kamar wasan tsalle-tsalle da sauran su.
4. Yawan hawan keke ko doki
5. Hawa jaki da dai sauran su.
Ya kamata iyaye su dinga hana yara mata irin wadannan matsalolin don haka haramun ne ya kawo wani mummunan zargi game da matarsa har idan ya same ta ba da murfin budurci ba. Ana iya samun matsala ma’aurata su sani cewa ba lallai bane su samu nasara a daren farko su domin gajiyar hada-hadar biki da fargabar yin wani muhimmin abu Na Karo Na farko Na iya haifar da kaduwar jiki har tasa ango yaji Ya kasa, don haka ba lallai bane ko dole sai an gabatar da ibadar aure a daren farko, in aka daga shi zuwa wani dare, bayan jiki Ya huta, abin yafi kayatarwa sannan ga sabon angon da ya san yayi sabo da zinar hannu, Ya kamata yayi kokarin dainawa a kalla wata uku kafin daren farko, kuma Ya sababbin ma’aurata su sani, haramun ne gare su yin tunane-tunanen alfasha kamar kallon finan-finan alfasha.
Menene Ladubban Daren Farko?
Bayan bayani kan Menene ake nufi da daren, za mu kara bayani kan menene ladubban daren farko da yake da muhimmanci duk ma'aurata su sani.
Da farko idan zaka shiga dakin amaryarka, zaka shiga ne da alwala. sannan zaka nemi dan wani abinci mai daraja, misali: kamar kaza ko tsire da sauransu idan ka shiga zaka umurceta itama taje tayi alwala sannan ku yi ma Allah godiya a bisa cika muku burinku da yayi, ku yi addu’o’in abisa kanku da dukkan al’ummar da suka amsa gayyatar ku suka halarci wajen daurin aurenku daga nan sai ka dafa kanta ko goshinta sannan ka karanta wannan addu'a kamar haka;
” ALLAHUMMA INNEE AS’ALUKA KHAIRAHA WA KHAIRA MA JABALTAHA ALAYYA WA A’UZUBIKA MIN SHARRIHA WA SHARRI MA JABALTAHA ALAIYAYA ( ko kuma ma jubilat alaiha )
( abu dawud Ya ruwaito DA ibnu maajah DA nisa’i )
Daga nan kuma sai ku ci wannan abinda ka shigo dashi ku dan sha wani abu amma ba’a so mutum yaci abu mai nauyi sosai a irin wannan lokacin. Daga nan kuma sai ku kusanci juna, tare da gabatar da ɗan wasanni da juna kafin ku fara gabatar da ibadar aure, kuma akwai addu’o’in da ake karantawa daidai lokaci jima’i kamar haka ;
“Allahumma jannibnash shaitan wajannibish -shaytana ma razaktana”
ANNABI ( S.A.W) yace “idan aka kaddara samun ciki a wannan saduwar to shaitan ba zai iya cutar dashi ba har abada ( bukhari DA muslim suka ruwaito ).
Wannan dai shine bayani kan menene daren farko da kuma menene ladubban daren farko. Da fatan sabbin ma'aurata sun ilimantu daga wannnan bayani. Allah ya tabbatar da zaman lafiya a gidajen aure, amin.