Me "Blood Pressure" ke nufi?

Me "Blood Pressure" ke nufi?
Me "Blood Pressure" ke nufi?


Blood Pressure(BP) shi ne awun batsewar jini a cikin jijiyoyin jini.


Daidaitacciyar batsewa ita ce lafiyayyar batsewa wace jiki zai iya amfana daga sinadaran da jinin ke ɗauke da su, kamar oksijin, sinadaran abinci, magani da sauransu.


Batsewar jini na iya hawa ko sauka saboda wasu lalurori ko matsaloli. Duka hawa ko saukar batsewar jini na iya janyo munanan illoli ga jiki, a wasu lokutan ma za su iya sanadiyar mutuwa.


Daga cikin lalurorin da ke janyo hawan batsewar jini akwai hawan jini, wato "hypertension". Hakan na faruwa saboda ƙaruwar batsewa jini a cikin jijiyoyin jini fiye da ƙima sakamakon cushewa ko taurin jijiyoyin jinin.


Ita kuwa kwalara, wato amai da gudawa, na daga cikin lalurorin da ke janyo saukar batsewar jini. Hakan na faruwa saboda raguwar ruwan jiki ta hanyar amai da gudawa.


Daga ƙarshe, daidaitacciyar batsewar jini, wato "Normal Blood Pressure" ita ce lafiyayyar batsewa da jiki ke buƙata. A yayin da hawa ko saukar batsewar jini barazana ce ga lafiya da rayuwa.


©Physiotherapy Hausa


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post