Manyan abubuwan da maza ke bukata daga wajen matansu |
Ansar karatun mu da mukai baya a kan tambayar JIGAJIGAN abubuwan da maza ke buqata fiye da saduwa a zamantakewar aure.
Duk yadda kika kai wajen kyau, wayewa, iya kwalliya, rangwada da yanga, taku, iya girki, gyaran jiki da gida, d sauransu. idan miji baya samun abubuwanda aka lissafo a kasa a wajen ki zaiyi wuya yaji daɗin zama dake ko kiji daɗin zama dashi.
Domin shi namiji yana matukar son yaga matar sa na yi masa wadannan abubuwan kamar haka;
1. Na ganin girma, kima da darajar sa a matsayin miji, shugaba kuma jagora
2. Ana masa matukar biyayya ga umurni da hanin sa.
3. Sa hankali da kula da al'amuran da ya shafi rayuwar sa.
4. Kokari wajen samar masa da farin ciki da nitsuwa
5. Yabo,karfafa masa da gode masa
6. Mace mai wadatan zuciya da karancin buri
7. Ba kawai saduwa ba, yana son ki kasance Mai samar masa da nishadi da shauqi a lokacin saduwa da zai samar masa da cikakken gamsuwa.
8. Hakuri da yi masa uzuri akan raunin sa
9. Mutunta iyayen sa.
10. Tausayi da rufa masa asiri akan rauni da babun sa.
11. Nisantar abunda zai na sa shi ɓacin rai. Wato kiyaye triggers din sa.
12. Kyautata mu'amala gareshi
13. Kiyaye amfani da buqata da raunin sa wajen cutar dashi.
14. Mai iya nishadantar dashi da hira da raha.
15. Kyautata kalamai gareshi.
16. Fahimtar yanayin sa kokari da hakuri wajen mu'amalantar sa yadda yake. (Acceptance)
17. Rike masa amana da Mutunta igiyar auren sa
18. Kiyaye masa dukiyar sa
19. kyautata masa zato
20. Kiyaye masa bincike da kwakwa a rayuwar sa.
21. Alfahari dashi. Etc.
Matuqar kika kiyaye wadannan kuma ki ka qawata su da irin su kwalliya, gyaran jiki da gida, iya girki etc. In sha Allah tsab zaki zauna lafiya da miji.
✍️ Fatimah Chikaire