Maganin Da Yake Rage wa Maza Sha'awa Da Ƙarfin Mazakuta |
Idan Kai Namiji Ne, Kuma Kana Da Aure, Kuma Kana Da Gyambon Ciki (Ulcer), Matso In Maka Wani Bayani Domin Ka Tsira Da Mutuncin Ka
Sanin kowa ne cewa yawanci magunguna suna da illar da ba'a so (Side Effects), wasu Illolin masu tasiri wasu marasa tasiri.
Maganin Ulcer CIMETIDINE (Tagamet) da Yadda Yake Shafar Lafiyar Jima'i Na Maza
Cimetidine, magani da ake amfani da shi don magance gyambon ciki da rage acid, yana iya shafar lafiyar jima'i na maza saboda tasirinsa kan sinadaran jiki da yadda jiki ke aiki.
Ko da yake Cimetidine yana da tasiri wajen magance matsalolin ciki, yana iya kawo cikas ga lafiyar jima'i na maza. Yin amfani da maganin cikin kulawar likita zai iya taimakawa wajen rage waɗannan illolin.
Ga yadda yake yi:
1. Rage Sha'awar Jima'i
Cimetidine na hana aikin sinadaran androgens (hormone na maza), yana rage testosterone, wanda zai iya rage sha'awar jima'i.
2. Matsalar Rashin Karfin Mazakuta (Erectile Dysfunction)
Rage yawan testosterone na iya haifar da matsala wajen samun ko riƙe karfin mazakuta.
3. Girman Nono (Gynecomastia)
Kun taɓa ganin maza da nono a kirji wanda ya ɗan tasa ko? Amfani da Cimetidine na dogon lokaci ko a manyan kwayoyi na iya haddasa girman nono ga maza saboda rashin daidaiton hormones.
4. Rage Ingancin Maniyyi
Cimetidine na iya rage yawan maniyyi da yadda suke motsawa, wanda zai iya shafar haihuwa.
Shawara
Idan ka lura da waɗannan illolin, ka tuntubi likitanka. Za a iya sauya maka magani ko rage yawan maganin da kake sha. Kada a yi amfani da Cimetidine na dogon lokaci sai dai idan likita ya bada umarni.
Sunana Pharmacist Musa A Bello Zaria, ina muku fatan alkhairi.