Ko kun san ana tauyewa mata haƙƙoƙinsu ta wani bangaren?

Ko kun san ana tauyewa mata haƙƙoƙinsu ta wani bangaren?

Ko kun san ana tauyewa mata haƙƙoƙinsu ta wani bangaren? 


Shiri ne da ke ƙoƙarin gayyato Mata 'yan Arewa: 'yan Makaranta, 'yan ƙwalisa, 'yan Gwagwarmaya, 'yan kasuwa da ma sauran fitattun Mata baki-ɗaya domin tattaunawa da su a kan: rayuwarsu, nasarori da ƙalubalen da suka fuskanta, da ma wasu muhimman shawarwarin da ake iya ji daga gare su, a kan al'amuran yau da kullum musamman waɗanda suka shafi Mata.


Yau a cikin Shirin, ina tare da babbar baƙuwa, Ummulkhairat Sulaiman Bakaree. Na yi farin ciki da kika amsa gayyatarmu, ina yi maki barka da zuwa, Masu karatu za su so jin Tarihin rayuwarki; Ma'ana Wace ce Ummulkhairat Sulaiman Bakaree?


UMMULKHAIRAT: Wa alaikumus Salam warahmatullah, Na gode sosai wa Shirin Zinariya da suka zaɓe ni a wannan rana a matsayin wacce za su yi hira da ita.


A taƙaice sunana Ummulkhairat Suleiman Bakaree daga jihar Taraba, ina da shekara 23 a duniya, 'yar fari da ƙanne bakwai' 5 maza 3 mata, da kuma iyayena, banda aure.


Nayi karatun primary school ɗina a model primary school daga 2003 zuwa 2008. 


Nayi secondary a Government Science senior secondary school daga 2008 zuwa 2013/2014.


Daga nan a shekarar 2014 na garzaya Remedial studies a College of nursing na Jalingo Taraba State. 2015 na samu Admission a College of nursing jalingo. Bisa ga wasu ƴan matsaloli da jama'ar Taraba suke facing na ƙabilanci da addinanci 2016 na fita daga makarantar. 


Daga nan na fara aiki As fisabilillah a Ummah clinic of Muslim council jalingo har na tsawon shekara ɗaya da rabi.


2018 February na samu Admission a college of nursing AtBu Teaching hospital Bauchi, Wanda a yanzu haka ina mataki na ƙarshe


MZM: Lokacin da kike ƙarama a burinki na ƙurciya me kike son ki zama?


UMMULKHAIRAT: A lokacin da nake ƙarama a gaskiya likitan Mata nake son na zama ma'ana (Gynaecologist)


MZM: Bayan kin girma wannan burin naki ya cika kuwa?


UMMULKHAIRAT: Wannan burin bai cika ba amma Alhamdulillah tun da har yanzu Ina cikin fannin kula da lafiyar ɗan Adam.


MZM: Idan aka cewa Mace 'Yar Arewa kasancewarki ke ma daga Arewar kike wane kallo kike yi Mata?


UMMULKHAIRAT: Idan aka cewa Mace Ƴar arewa ina mata kallon ƴar uwata Mace, kamila, Mai mutunci, Mai tarbiya, Mai kunya, wacce ta san ya kamata.


MZM: Ko kina ganin akwai wasu haƙƙoƙi da ake tauyewa 'ya'ya Mata a rayuwarsu?


UMMULKHAIRAT: Ƙwarai da gaske ana tauyewa Mata haƙƙoƙinsu ta wasu ɓangaren, domin za kaga yarinya ta taso da ilimi da kuma burin zama wani abun taimako wa al'umma amma iyayenta su aure ne a gabansu, inda wasu suke barin yaran su tsaya a matakin primary wasu kuma secondary kawai, wasu kuma basa barin yaran suyi boko ko kaɗan domin a ganinsu duk mace da tayi Boko ƴar bariki ce.


Abun takaicin ma wasu auren dole ake musu, wasu kamma da sa'o'in iyayensu maza ake aura masu, ko kuma yaran basu Kai zaman aure ba ake aurar dasu.


Sai ta ɓangaren Mazajen wasu Mazajenmu a Arewa sun ɗauki mace kamar ba komai ba, sun ɗauke yara Mata Kamar karnukan su, su musu tsawa lokacin da suka so, su hana su su kuma saka su, lokacin da su ke so koda kuwa basa ra'ayin hakan. Wanda kuma haka ba daidai bane domin Allah ya martaba kowane ɗan Adam. Wasu mazan idan suka samu mace ma'aikaciya har aiki suna iya hana ta ba tare da wani dalili ba, kuma aikin nan zai iya taimakansu dukkansu.


Abubuwan dai suna da yawa idan za mu yi magana a kansu ɗaya bayan ɗaya zamu iya kwana ban gama lissafosu ba.


MZM: Wace Mace ce kike son zama kamar ita, ko kuma take burgeki, kuma dan me?


UMMULKHAIRAT: Mamata, mamata Nihad Sulaiman ita take burgeni a rayuwa kuma nake burin Zama kamar ita. Domin mace ce a tsaye, ma'aikaciya wacce take taimakawa jama'a Ko da bata san su ba, mace ce wacce tana iya bawa wasu matan shawarwarin yadda zasu tafiyar da al'amuransu na yau da kullum. Akwai wani al'amari da tayi a gabana kuma ya burgeni, ta sakani na rakata gaisuwa a asibiti, muka ɗan zauna da wasu ƴan uwanmu a tabarma a wajen ward, sai taji wata Mata a gefe tana bada labarin yanayin kuɗin da suka kashe sannan kuma yanzu haka an rubuta magani babu kuɗi, infact ba su da abinci, kuɗin da ya rage a hannunta wato mamata 2000 haka matar nan ta cire ta miƙa musu,  mu kuma muka taka da ƙafa muka koma gida domin bamu da kuɗin adaidaita. Kullum idan na tuna wannan ina ƙara roƙon Allah ya bani ikon yin haka koma fiye da hakan.


MZM: Wace rawa kike ganin 'ya Mace na takawa idan ta shiga ƙungiya?


UMMULKHAIRAT: Ɗiya Mace tana taka rawa sosai a ƙungiya domin idan muka lura ai Mata sune ginshiƙin al'umma, ga tausayi ga kuma sanin ya kamata. 


-Ummulkhairat Suleiman Bakaree



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post