Ɗisowa ko ƙwacewar fitsari ce matsalarki/ka?

Ɗisowa ko ƙwacewar fitsari ce matsalarki/ka?
Ɗisowa ko ƙwacewar fitsari ce matsalarki/ka? 



Ɗisowar ko ƙwacewar fitsari ga maza da mata na daga cikin matsalolin da ke barazana ga ibada, tsabtar jiki da walwala.


Ɗisowa ko ƙwacewar fitsari musamman yayin ayyukan yunƙuri na nuni da raunin tsokokin shimfiɗar ƙugu.


Ayyukan yunƙuri da ke sanya fitsari ya ɗiso ko ya ƙwace sun haɗa da: dariya, atishawa, hamma, tari, gudu ko yunƙurin ɗaga kayan nauyi.


Idan kana fama da ɗisowa ko ƙwacewar fitsari yayin waɗannan ayyuka hakan na nuni da rauni ko rashin ƙwarin tsokokin shimfiɗar ƙugu.


Tsokokin shimfiɗar ƙugu suna ɗauke da tsokokin maɗaurin jakar fitsari. Saboda haka, raunin tsokokin shimfiɗar ƙugu na janyo tsokokin maɗaurin jakar fitsari su yi rauni.


Idan maɗaurin jakar fitsari ya yi rauni, hakan zai haddasa ɗisowa ko ƙwacewar fitsari yayin da aka takura jakar fitsari yayin ayyukan yunƙuri da aka ambata a sama.


Abubuwan da ke ƙara haɗarin samun lalurar ƙwacewar fitsari sun haɗa da: goyon ciki, haihuwa, doguwar naƙuda, tangarɗar naƙuda, ƙiba ko teɓa, matsanancin tari tsawon lokaci, bugu ga ƙugu, matsalolin da ke biyo bayan tiyatar ƙugu da dai sauransu.


Idan kina / kana da matsalar ɗisowa ko ƙwacewar fitsari, tuntuɓi likitan fisiyo a yau.


© Physiotherapy Hausa


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post