Illolin istimna'i (wasa da al'aura) ga ma'aurata da hanyoyin guje musu |
Biyawa kai bukata ta hanyar istimna'i wato( wasa da al'aura) masturbation da turanci, ko kuwa "istimna'i" din da harshen larabci, yana nufin duk wata hanya da mutum zai bi don ya samarwa kanshi biyan bukata wato zubar da maniyyi ba tare da saduwa tsakanin jinsin mace da namiji ba.
Tarihi ya nuna cewa masturbation(wasa da al'aura) ya samo asali ne tun zamanin annabtan Annabi Luth (Lud), lokacin da jama'an wancan lokacin suka shiga cikin bala'in luwadi a tsakanin su, Matsalar da ta zama ruwan dare game duniya tsakanin mata da maza marasa aure wani lokacin ma harda masu auren.
Masana a fannin kiwon lafiya a mataki daban-daban sun sha gwagwarmaya wajen yakar wannan dabi'a a tsakanin al'umma lura da iri-iren illolin da wannan al'ada ke tattare dashi ga zamantakewar ma'aurata da kuma lafiyar su.
A likitance masana sun bayyana cewa istisma'i ba za'a kira shi da suna ciwo ba, haka kuma babu ainihin maganin da zai kawar da wannan al'amari kai tsaye illa canza ko sauya tunanin jama'a, musamman wadanda suka rigaya suka afka cikin wannan dabi'ar. A bisa kula da illolin da wannan al'adar zai iya yi ga rayuwar bil'adama, masanan sun bayyana wasu daga cikin illolinsa, bayan ga haramcinsa a addinin Musulunci da ma na Kiristanci, da dama kamar haka:
Iillar istimna'i ga lafiyar bil'adama(wasa da al'aura)
Masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa, duk sanda bil'adama ya fitar da maniyyi, wahalar da jiki kan yi na dai-dai da gudun kilometer 13 (13km) wasu na iya wannan dabi'ar sau 3 ko fiye da haka a wuni, kunga a nan dole matsaloli su biyo baya kamar ciwon jiki da shanyewar hannaye da kuma rama da rashin kuzari. A bisa wannan dai masanan sun tabbatar da wannan dabi'ar na ruguza daukacin tsarin jikin bil'adama.
Masanan har ila yau, sun bayyana cewa wannan dabi'ar kan jawo ciwon zuciya ga mai yin ta. Ya kan jawo rashin karfin gaba. Duk mai wannan dabi'ar yau da gobe zai rasa karfin gabanshi kwata-kwata. Har ila yau an tabbatar da cewa duk mai dabi'ar aikata Istimna'i lallai ne sai ya kamu da cutar sanyin mara (gonorrhea) wanda kan iya illata shi.
Illoin istimna'i (wasa da al'aura) ga zamantakewar ma'aurata
Yana iya haifar da kiyayya da zargi tsakanin mata da miji. Duk ma'auratan da daya daga cikin su ke wannan dabi'ar to tabbas ba zai iya gamsar da daya ba ta hanyar jima'i. Misali, idan miji ya fita aiki yabar matar shi gida sai tayi istimna'i, idan ya dawo aiki yana bukatar ta da jima'i, ba zata kulashi ba saboda ita ta riga ta zubar da sha'awarta, hakazalika na mijin. Kuma ko da jima'i ya kasance tsakani, to za'a samu matsalar rashin jin dadin saduwa saboda waccan dabi'ar ta gusar da sha'awar aboki ko abokiyar saduwa.
Masana sun kara bayyana cewa wanna dabi'ar ta Istimna'i (wasa da al'aura) bisa binciken su kan iya hana haihuwa. Ya tabbata cewa namiji ba zai iya samar da ciki ba har sai an samu kashi 60 zuwa 70 cikin dari na yayan maniyyi, wanda kuma yayan maniyyin ba zasu kammala hakan ba sai mutun ya kasance lafiyayye kuma mai kuzari. Wanda duk mai wannan dabi'ar ana iya samun shi ko samun ta da karancin kuzari wanda hakan na iya hana su haihuwa.
Shawara ta yadda za'a iya gujewa dabi'ar Istimna'i (wasa da al'aura)
1) Da farko idan mutun ya tsinci kanshi cikin wannan dabi'ar kuma yana bukatar dainawa, to, sai ya kudurta a cikinn zuciyarsa cewa zai daina saboda dabi'ar na da makutar wuyar dainawa muddin ta yi wa mutun katutu.
2) Mutum yayi kokarin aure idan da hali, sannan Ka daina kadaita a dakinka ko gidanka, ka rika shiga mutane. Dan mafi yawa kadaita ke sa wasu mutane wannan dabiar. A guji shan kwayar da zata tada sha'awar jima'i.
3) A guji yawan kallon ababen da zai tada sha'awa, hoto ko bidiyo, kana a guji yawan zantutukan batsa wanda suma kan haifar da sha'awa.
A yawaita jin karatu ko wa'azi a ko da yaushe. Domin yin hakan za su dauke hankalinka daga daina tunanin aikata Istimna'i (wasa da al'aura)
Idan aka kiyaye wadannan abubuwa, in Allah ya yarda duk mai dabi'ar wasa da al'aura zai iya dainawa. Allah Ya sa mu dace.