Illar Auren Kyakkyawar Mace, Yafi Rashin Aure Firgitarwa A Halin Yanzu |
Kashi 98% Na Matasa A Yanzu Kowa Burin Shi Ya Auri Mace Mai Kyau, Duk Da Mafi Yawancin Su Basu San ILLar Dake Tattare Da hakan ba.
Mafi Yawancin Mata Masu Kyau, Sunada Wani Hali na Masanman A Matsayin Su Na Kyawawa. Kadan Daga Ciki sune:
Ita Mace Mai Kyau A Mu'amala Ta Aure Kullin Gani Take Taimakon Ka Tayi Ta Aure Ka
Mafi Yawancin Mata Masu Kyau Basu Cika Biyayya Ga Mijin Su Yadda Ya Kamata Ba
Mace Mai Kyau Kullin Gani Take Idanma Ka Rabu Da Ita Wasu Mazan Sunanan Suna Jiranta
Mata Masu Kyau Basu Cika Zaman Aure Ba, Saboda Wannan Kyan Nasu Shi Yake Ziga su Su yi Ta yiwa Mazaje Rawan Kai
Kaso 75% Na Zawaran Da Muke Dashi A Yanzu Idan Ka Duba Zakaga Kyawawa Ne, Ka Taba Tambayar Kanka Meyasa?.
Da'ace Matasa Yan Uwana Zasu Gane Ko Kuma Da Za Suji Shawarata, Da Sun Guji Auren Macen Da Kyanta Ya Bayyana Ga Kowa.
Ka Dage Da Addu'ar Samun Mata Ta Gari Sannan Ka Auri Mace Ta Tsakiya A Wurin Kyan Halitta Da Sura.
Akwai Amfanun Auren Kyakkyawan Mace, Shima Yananan Tafe In Sha Allah, Allah Ya Datar Damu.
YAHAYA ADAM KUBAU