Halayyar Da Mace Ke Yi Idan Bata Samun Gamsuwa A Jima'ince

Halayyar Da Mace Ke Yi Idan Bata Samun Gamsuwa A Jima'ince

Halayyar Da Mace Ke Yi Idan Bata Samun Gamsuwa A Jima'ince


Ka taba tashi da safe ka samu matarka ta shirya maka abun karin kummalo mai rai da lafiya tun kafin ka tashi, tazo cikin kunnenka ta kiraka da suna mai dadi cike da soyayya ta tasheka domin ka shirya ka karya kummalon ka?


Ka taba tashi da safe kaga matarka tana kumbure - kumbure gaisuwa safe ma sai kaine zakai mata kuma ta amsa maka ciki-ciki, ka tambayi abincin ka na karin kummalo tace gashi can ka dauka?


Idan dukkanin ku biyu amsar ku e ne, to hakan yana da alaka ne da yadda kuka sarrafa matanku cikin dare.


Ba ina nufin dole sai a cikin dare ake saduwa da mata ba, sai dai a wannan lokacin ne magidanta suka fi samun natsuwar yin hakan.


Mace muddin ka gamsar da ita, annashuwa ta, kwanciyar hankalinta dama kaunarka dukkaninsu ninkawa suke yi. Haka nan akasin hakan.


Kamar yadda muka sani ba duk mata bane suke yin zuwan kai ba. Amma dukkanin mata suna samun gamsuwa ba tare da sun yi zuwan kai ba. Haka nan ma maza ba sai namiji ya kawo ne yake jin dadin Jima'i ba.


Duk macen da bata samun gamshenshen Jima'i a gidan miji a gaskiya za a iya samunta tana cikin tashin hankali da rashin natsuwa. Ga yawan damuwa da toshewar basira taji ta tsani kanta da kanta ta kasa ma fahimtar zaman auren da take yi. Ko da kuwa bata rasa komai na rayuwa a gidan mijinta ba.


Mace Da zata rasa komai a gidan miji amma gamsuwa na Jima'i sai ta ture, wannan matar sai tafi wacce take gidan mawadaci amma babu gamsuwa kyaun gani da walwala.


Rashin gamsuwa a Jima'ince ga mata ba karamin nakasa su hakan yake ba. Gara ma ace mace bata yin Jima'i ba da ayi Jima'in amma a kasa gamsar da ita.


A wannan karnin har yanzu ana samun mazan da suke daukar cewa yiwa mace ciki ai gamsar da ita ne. Wannan ba haka yake ba. Mace na iya yin ciki a wannan zamanin ma ba sai namiji ya kusan ceta ba. Don haka shigar ciki daban, gamsar da mace daban.


Yana da kyau duk wani magidanci ya fahimci gamsar da matarsa a lokacin Jima'i wajibi ne kamar yadda sauran wajibai a aure yake kansa. Tsoma ka cire bai zama hanyar gamsar da mace, yin awanni kana Jima'i da mace ba shi zai sa ta gamsuwa ba. Zuwan kai fiye da sau goma ba ya sa mace jin dadin Jima'i. Kawai yi kokarin fahimtar mai matarka tafi so yayin saduwa ka mata shi har sai ita da kanta tace ta gamsu.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post