Gidan aure kamar kabari ne kowace mace da halinta zata je |
Hakika a wannan zamani yana daga cikin abinda ya shigar da mafiya yawan Mata cikin gidajen su na Aure NASABA da KYAU da suke dashi.
Sai dai wasu matan kuma DABI'AR SU da HALAYYAR su a gidajen mazajen su yana nan yana fiddasu daga gidan aure.
Yan 'Uwa na MATA ku kula wajen kiyaye hakkin zaman aure. Kada ku rudu da kyaun da kuke da shi ko kuna tinkaho da nasabar ku. Ku mutum ta abokan zama, sanna ku kyautata zaman auren ku.
Hakanan 'Yan Uwa na MAZA mu kiyaye kada kyawun mace yayi mana tasiri sama da addinin ta, muyi kokari ana binciko mai kula da addini da halayya ta gari da dabi'a mai kyau kafin ayi aure.
Tabbas ba haramun bane Ka nemi mace kyakkyawa, amma fa ka tabbatar tana da tarbiyya. Idan ko ba haka ba to ka sani kyaun zai shigar da ita gidan ka, amma fa gurbataccen tarbiyya zai fidda ita.
Duk mace mai ilimi da nasaba mai daraja in taki aiki da ilimin ta, sannan taki kyautata halin ta a zaman auren ta to ta zamo kara da kiyashi..
Allah Yakawo mana saukin yawan sake-saken aure da ake fama dashi, amin