Falalar Auren Namiji Nagari |
بسم الله الرحمن الرحيم
Ga wasu alfanu da mace zata amfanu dasu idan Allah yayimata rabon Auren miji NAGARI
1 Idan mace ta auri miji nagari kuma ta aureshi saboda ALLAH tabbas za ta kasance cikin farin ciki da walwalar gangar jiki da ruhi saboda zai zama mata jigo bango majingina ta yadda zai bata cikakkiyar kulawa saboda dama shi miji nagari ya iya kula gami da bawa mace hakkinta iya gwargwado
2 Duk macen da tayi gamdakatar da samun Namijin kwarai a matsayin maigidanta Tabbas Zata rayu cikin cikakkiyar nutsuwa saboda zai sadaukar da lokacinsa domin ya saurari dukkan damuwar ta Saboda ya kwantar da hankalinta gami da samar da farin ciki a gareta.
3 Miji NAGARI Aurensa ribane kuma rabone saboda idan kina gidanshi in sha ALLAH zaiyi iyakar kokarinsa dan ganin cewa ya ciyar dake halal komin kankantarsa ya kuma gujewa kawomuku haramun komin yawansa
4 Yana daga cikin babban rabo game da auren mijin kwarai shine a cikin unguwa babu wanda ya isa yayiwa ya'yanki gorin uba domin shi koda yaushe burinshi shine yaga ya'yanku sun yi tarbiya kuma sun zama yaran kirki wadanda musulunci da musulmi za su yi alfahari da samunsu
5 Auren Miji NAGARI kwanciyar hankaline ga dukkan macen da ta samu, domin Shi mutum ne wanda zayi iyakar kokarinsa bisa taimakon Allah dan ganin bai tauye hakkin matarsa ba da yake kansa
6 Idan har kinason kiga yadda ake tausayawa mace ake tarairayar mace ake damuwa da damuwar mace to wannan duk sai A wajen mijin kwarai.
7 Daga karshe dai Shi namiji NAGARI baya auren mace domin wata Niimar duniya mai gushewa kamar Kyau, Nasaba, Kudi da sauransu yana auren macene Saboda ALLAH kadai domin shi yasan cewa yin aure domin ALLAH kadai shine zaisa aci riba da kuma amfaninsa.
Dan haka shi damuwarshi shine kawai kikasance mai addini da kyawawan dabi'u Anan ne zakiga yadda yake matukar nuna so da kauna agareki hadi da nuna kishi akanki
Yan uwa mata masu Albarka ku dage da Addu'a ku kuma kama kanku ku zama NAGARI domin samun irin wannan jajirtaccen.