Dalilan Dake Tilastawa Maza Karin Aure — Android Pols

Dalilan Dake Tilastawa Maza Karin Aure
Dalilan Dake Tilastawa Maza Karin Aure


Duk da halalcin da yin mata fiye da biyu yake da shi a tsari na addinin islama, ba duk maza Musulmai bane suke da sha'awar auren mace fiye da guda ba. Wasu mazan karin auren yakan zo musu ne a babu yadda suka iya, yayin da wasu kuwa suna maida aure abun wasa. 


Wasu mazan sun tsani yin aure su yi saki, mai makon hakan sai kawai su kara wani auren idan suka fahimci wanda suke dashi a yanzu akwai takura ko cutarwa. Kafin ka zargi namiji akan karin aure, ka fara sanin dalilin daya sa zai kara ko ya Kara tukun. Ga wasu dalilan da ke sa wasu mazan suke kara aure domin zama da mace fiye da guda. 


1: Rashin Godiya:

Akwai wasu matan duk abunda mazansu za su yi musu na kyautatawa ba za su taba nuna godiyarsu da kokarin mazan ba. Sai ma nuna musu gazawarsu ta nuna abunda akayi da ba hakan aka yi musu ba.


Nunawa mutum godiya yana daya daga cikin rukunin abunda Allah Yake so a yi masa a lokacin da ya yiwa mutum wani kyauta. Hakan shi ma mutum yana so a duk lokacin da yayi abun bajinta a yaba masa domin gaba yaji dadin kara yin fiye da hakan.


Wasu mazan ta hanyar da suke ganin zasu huce takaicin rashin godiyan da matansu ke masu shi ne ta hanyar kara wata matan.


2: Almunbazzaranci:

Akwai matan da duk irin tanadin da maigida zai yi a gidansa na kudi, kayan abinci da sauran abubuwan amfani, sai sun wulakanta su wasu ma yin kyautar suke yi ba tare da amincewar miji ba.


Tabbas irin wadannan matan na matukar hasala mazansu su har daga bisani su yi tunanin sake auren wacce za ta kular masa da abubuwan da zai bari a karkashin kulawar ta. 


3: Tsiwa:

Akwai matan da muddin kana tare dasu bakada kwanciyar hankali har sai lokacin da ka baro gida. Haka idan zaka koma gida gabanka na faduwa saboda yawan masifansu, tsiwa da mita. 


Hakan yake sa mazan da suka samu kansu tsumdum da auren irin wadannan matan dole yake sa su kara wani auren domin samawa kansu lafiya. 


4: Rashin Sirri:

Akwai matan da duk halin da miji yake ciki na kunci basu damu ba. Kuma dukkan sirrin mijin su basa boyewa kawaye ko dangi, hakan ke tilasta namiji ya kara aure. 


Wannan wasu ne daga cikin dalilan dake sa mazan aure su yi tunanin karin aure, domin irin abubuwan da matansu ke yi musu. Da fatan matan aure masu wulakanta mazajensu za su kiyaye. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post