Aure lokaci ne ƴar uwa me yasa zaki ɗaga hankalinki?

Aure lokaci ne ƴar uwa me yasa zaki ɗaga hankalinki?
Aure lokaci ne ƴar uwa me yasa zaki ɗaga hankalinki? 


Kada ki ga aurenki ya taso gadan-gadan sai wani dalili yasa akace an fasa auren ko da auren ya taso sai ku yi ta rabuwa da mijin da zaki aura, kada kice kamar banida sa'a idan ma kina wannan tunanin ki daina. ki tuna Allah ne mai tsara komai kowa da irin jarrabawar da Allah yake yi masa. Ki ji a ranki cewa Allah ya tanadar miki canji mafi Alkhairi. 


Haka kuma kada ki ce ko asiri akemin naƙi aure kada kice ko shedanu ne suke son hanani aure. ki yi ta zarge-zargen da babu kyau. Ki tuna ba wanda ya 'isa ya hanaki auren indai lokacin yinki yayi ki gane ki fahimta ko shedanu masu hana auren gareki indai lokacin auren yayi sai Allah ya kawar da matsalar ayi auren wadda ba'a taba maganar auren ba. 


Kada ki ce ni fa nagaji da zaman gidannan kowa na samu gwara in aura koba bincike ko ki fara yawan neman miji ko ta halin ƙaƙa. Shin idan kika ce kowa zaki aura kinsan yaya halinshi yake? ki aura kizo daga baya kina nadama. Wata fa gaggawa da rashin haƙuri Matsala take janyowa babba Ki tuna Allah yasan dake kuma wani jinkirin Alkhairi ne idan kikai haƙuri sai kiga Allah ya baki miji nagari ta inda bakya zato ke dai kiyita Addu'ar Allah yakawo miki miji na ƙwarai. Kuma idan kin samu mijin ma kafin ki amince masa kiyi istikhara (Addu'ar Neman Zaɓin Allah) ki yi ta da kanki ba wai a yi miki ba.


An karbo Daga jabir Bin Abdullahi(R.A) Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana koya mana istikhara a kowane lamari kamar yanda yake koya mana Surah ta Al'qur'ani.


 Kuma babu kyau ka ba wa wani yayi maka istikhara. Kuma da yawa rashin yin istikhara kafin Aure zata kasance na haifar da wasu matsalolin da ake samu bayan yin Aure.


Kada kije gurin boka ko malamin duba kice yaduba miki yaga yaushe zakiyi aure ko kice gawani kinaso shi ba ya sonki yasa ya soki dole haƙiƙa idan kikaje kinyi shirka (hada Allah dawani) kuma zakiyi danasani daga baya  


Allah maɗaukakin sarki yace: ku bautawa Allah Kada ku sanya masa kishiya (Surah An-nisa Aya 36)


✍️Zainab Abdullahi Haladu



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post