Amfanin nonan rakumi ga mata da maza |
Nonon rakumi dai amfaninsa ba zai iya lissafuwa ba, domin idan muka ce za mu bayyana amfanin da yake yi ga jikin dan adam sai mu shafe tsawon lokaci. Amma dai za mu kawo muku wasu daga cikin Muhimman amfanin sa ga maza da mata.
Amfanin nonan rakumi ga mata
Wannan hadin yana taimakawa ga mata gaya dangane da abinda zaman takewar aure, musamman kara niima da sauran su.
Domin yin wannnan hadin akwai abubuwan da ake nema don a yi kamar haka:
Zaki samu wadannan abubuwa kamar hak
(1) No-non rakumi Mara hadi ko kadan.
(2) aya
(3) gero.
(4) kwakwa.
(5) dabino bushashshe.
(6) sansami
Hanyar da zaa hada zaa nika aya, a nika gero, a nika dabino da wannan kwakwa, amma ayar kafin a nika ana bukatar a soya ta kadan, idan akayi garin wadannan Magungunan Sai a hada waje daya.
Sai a kawo wannan nonon rakumi a zuba kadan ana gaurayawa har sai ya hade sosai ta yadda kada a cika daga nan ana bukatar za'a busar dashi.
Amfanin nonan rakumi ga maza
Bayan ya bushe za'a Kara nikawa ko a daka Sai a dinga shansa da madara ko a ruwan shayi, insha Allah wannan zai taimaka sosai wajen bada niima da kuma magani.
Dangane da maza kuma zaka iya samun nonon rakumi mai kyau Mara hadi da kuma fitsarin sa, da kuma Zuma. Sai a hada nonon dan kadan da fitsarin kadan da Zuma ka gauraya ka shanye.
Ko kuma kahada da Zuma da fitsarin rakumi kadan, da nonon sa kadan sai ka zuba gishiri kadan ka gauraya kasha wannan yana taimakawa sosai ga mazaje wajen bada kuzari.
Amma idan ka samo marasa kyau to bazaa samu wannan faida ba, da fatan zaa kiyaye.
Bayan haka Kamar yadda ake yawan tambaya akan matsalolin da suka shafi maza maganar karfi, da Kara kuzari, zaka iya samun garin kuka Mara hadi, ka hada da Kanin fari, ko kayan yaji ka nike ka dinga sha da ruwa hakanan, ko ruwan shayi wannan Shima yana taimakawa sosai.
Bayan haka masu matsalar ciwon sikla musamman a lokacin sanyi matsalar tana yawan tashi, Kamar yadda wasu suka jarraba idan aka samu nonon rakumi, da kuma fitsarin sa wadanda basuda hadi akayi amfani dashi, Kamar murfin magani, za'a rika sha sau uku a rana, nonon Kamar Karamin kofin yara sau daya a rana, bayan haka za'a yi ma yaron wanka sannan a shafa masa fitsarin rakumi ayi Kamar haka na sati uku idan Allah swt. Yasa anyi bisa dace zaa iya samun sauki ko a sami waraka, wannnan sune daga cikin Amfanin nonan rakumi ga maza da mata.
Dafatan Allah taala yabamu da cewa Allahumma Ameen.
Rahamaniyya Islamic medicine and research Center Funtua Katsina State.