Abubuwan da ya dace ku sani gameda jijiyoyin laka

Abubuwan da ya dace ku sani gameda jijiyoyin laka
jijiyoyin laka


Ba ƙurji ba ne! Tsagawa na iya lahani ga laka ko jijiyoyin laka 


Daga cikin tawayar da a kan haifi jarirai da ita akwai tawayar laka da jijiyoyin laka. Yayin girman sassan jikin tayi a cikin uwa, halittar laka da jijiyoyin laka ba su kai ga cika yadda ya kamata ba. Saboda haka, ƙashin gadon baya zai yi wabi a daidai wurin. Sakamakon haka, sai laka ko jijiyoyin laka tare da ruwan laka su yi bulli waje kamar ƙari ko ƙurji a gadon baya. 


Alamomin tawayar sun haɗa da:


1. Rauni ko rashin ƙwarin ƙafafu.


2. Matsalolin fitsari ko bahaya.


3. Farfaɗiya.


4. Matsalolin numfashi da sauransu. 


Sabuban tawayar


Babu wani takamaiman sababi da aka sani wanda ke haddasa wannan matsala kai tsaye. Sai dai, ana alaƙanta sababin da gamayyar tasirin muhalli da dangi ko kuma ƙarancin sinadarin vitamin B9, wato folic acid, yayin goyon ciki.


Abin sha'awa game da wannan tawaya shi ne, ana iya gano tawayar tun jariri yana ciki ta hanyar yin hoto — sikanin, musamman ga mata masu zuwa awu asibiti yayin goyon ciki.


Haka nan, ana iya yin tiyata domin gyara tawayar tun jariri yana ciki ko kuma bayan haihuwa.


Daga cikin matakan kariya daga tawayar akwai: 


1. Karbar magungunan awun ciki: Magungunan awun ciki sun ƙunshi sinadaran ƙarin jini da sinadarin vitamins waɗanda ke taimakawa wajen rage haɗarin haihuwar jarirai masu tawaya.


2. Cin sinadarin folic acid (vitamin B9): Korayen ganyayyaki, kwanduwar kwai, hatsi da sauransu suna ɗauke da folic acid.


Game da jariran da ake haifar su a gida kuwa, da zarar an lura da wannan tawaya tare da waɗannan alamomi, to a garzaya asibiti domin ganin likita. Sannan kada a yi kasadar bulawa ko tsagawa ko kuma kai wa wanzami domin cirewa. Ba ƙari ba ne! Ba kuma ƙurji ba ne!


Game da raunin ƙafafu kuwa, likitocin fisiyo ne ke kula da matsalolin raunin ƙafafu da irin waɗannan yara ke zuwa da su har su iya tsaiwa da tafiya.


© Physiotherapy Hausa

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post