Abinda ya kamata duk mace ta kula dasu kafin tayi aure — Android Pols

Abinda ya kamata duk mace ta kula dasu kafin tayi aure
Abinda ya kamata duk mace ta kula dasu kafin tayi aure 


Yar uwata zo na baki shawara Kyauta 


Idan kina son kiji dadin zaman gidan aure, ki samu miji nagari wanda zaki samu  ingantacciyar rayuwa a gidan zaman auren ki, ki bi wadannan matakan guda bakwai (7)


(1) yar'uwata kibi Allah, ki kyautata Alakarki da mahaliccinki, ki bauta Masa iyakar iyawarki, ki kuma kasance kina bin dukkan umarce-umarcen Allah madaukakin sarki, sannan kuma ki nisanci dukkan hane-hanensa.


(2) Yar'uwata kibi koyarwar manzon Allah (S,A,W) kuma kiso manzon Allah (S,A,W) sama da kanki da kuma mahaifanki, kuma kiyi koyi da dukkan dabi'unsa, Kuma kiso dukkan iyalansa, kuma kiyi koyi da sahabbansa kuma kiso su.


(3) 'Yar'uwata ki kyautatawa mahaifanki ki girmamasu Kuma ki rika yi masu addu'a lokaci bayan lokaci, kada ki Zama Mai bijire musu, domin sun fi kowa kaunar ki. 


(4) 'Yar'uwata ki girmama bayin Allah kada ki wulakanta kowa ki dauki kowa da daraja sannan ki zama Mai fadin daddar magana ga kowa wadda zata saka bayin Allah farin ciki. Domin Annabi (S,A,W) yace:- magana mai dadi ma sadaka ce. 


(5) 'Yar'uwa ta ki zama nagartacciya mace Mai addini da illmi da tarbiyya wadda za ta zama abin sha'awa ga kowa kuma abin koyi, sannan ki kyautata dabi'unki. 


(6) 'Yar'uwa ta ki ci gaba da Neman zabin Allah a rayuwanki a dukkan lamurranki, Kuma kada ki biye ma rudun duniya kawai dai ki bi Allah.


(7) 'Yar'uwa ta ke mace ce Mai kima da daraja, da Kamala, don haka ya dace ki tsaya ki natsu wajen zabar abokin zama, Kuma ki nemi taimakon Allah. 


(8) 'Yar'uwata nagartacciya ke fah kyakkyawar zinariyar ce, Ina Maki fatan alkhairi, Allah yabaki miji nagari Mai addini nagartacce. 


'Yar'uwata kibi Allah sai ki zauna lafiya, a matsayina na mai karamin sani, wato mai karancin ilimi, ina rokon Allah ta'alah ya gafartamin zunubaina dukkan inda nayi kuskure, sannan ya bani ladar abinda na fada dai-dai, Nagode 'yan' Uwa. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post