Yadda Zina tai yawa a dalilin Tsadar aure ya a Kasar Hausa |
Ni yanzu ba wata wacce za ai Zina da ýarta na tausaya mata.
Kullum abubuwa na ƙara tsada amma an dage idan za a yi aure sai anyi yadda ake yi a baya. Idan sadaki ya zama dole wannan tsinannan kuɗin gaisuwar iyayen a'ina ya samo asali?
Sadaki 150k ko 200k wasuma har 500k,
Gaisuwar iyaye 50k wasu 100k wasu har 150k,
Lefe 500k ko 700k wasuma har 1m,
ZINA dubu akan dubu daya, wata ma kana saya mata abinci an wuce wajen. Wata ma kyauta zakayi zinar da ita domin itama mabukaciya ce.
Matuƙar ba mu gyara ba, ba mu bi koyarwan addini ba mun rinƙa ganin ba daidai ba kenan har bisa Mahadi. Ana ta zina da ýaýanku ba ku sani ba, yara sun san duk wani maganin da zai hana ɗaukar ciki ku kuna can gida kuna Wallahi sai an biya 200k sadakin Larai, Larai kuma ɗazu wani gaye ya bata 1k yai abun da ake jiran sai an biya 200k.
Ita dai Zina mai yinta ba ruwansa da ciyar da yarinya ko yi mata tufafi. Amma mijinta duk wata ɗawainiyarta ta na kansa. Don haka ya rage naku na ku taimaki kan ku da ýaýanku
Meye zai Hana Kawai in yarinya ta samu Mai son ta, ku saukaka masa a auren domin ya samu jarin da zai iya riketa bayan auren, da yawan samari tsadar aure ke hanasu yin auren, a wannan tsadar rayuwa da ake ciki abun kayi murna ne idan Yar ka ta samu mijin aure, domin wallahi wani ko kyauta aka bashi mace yanzu bazai karba ba, saboda yanayin kasar
Kodai ku yafe lefe da Al'adu da sauransu ko Kuma Yaranku mata su rasa mijin aure daga baya gayu Suyi ta zuwa suna lalatasu a gidajen iyayensu, tunda sha'awa bata da magani sai aure, aure Kuma ko a 10k ka bayar da auren Yar ka ga wani wlh bakayi asara ba Indai shi din mutumin kirki ne Mai sana'a
A duba Surah mai numbr 66, Suratul Tahrim Aya ta 6. Allah yace ku tsare kanku da na ýaýanku daga shiga wuta zuwa ƙarshe.
Allah ka shiryemu. Allah sa mu gane mu gyara Îbràhîm Àssàlàfîyàfîy