Yadda son auren namiji mai kudi ke jefa 'yan mata halaka a wannnan zamanin |
Kada ki kuskura idonki ya rufe, ki daina mayar da kudi ma'aunin gane mutumin kirki ko masoyi na gaskiya, wanda ya shirya yaudarar ki ma zai iya kashe miki kudi ko nawane domin ya yaudare ki.
Mata da yawa musamman a wannnan zamanin suna baiwa namiji mai kudi muhimmanci fiye da mutunuci da tarbiyyarsa da kuma yadda zai kula dake a zamantakewar aure.
Mata dayawa sun shiga matsala sakamakom mugun son kudi da sa kudi a matsayin hanyar da suke iya gane masoyi na gaskiya.
Mata dayawa sun rasa soyayyar gaskiya a dalilin tsabar son kudi, mata dayawa sun fada hannun wadanda basu dace da su ba kwalamar son auren miji mai kudi.
Shawara gare ku 'yan mata yayin zaben mijin aure
Duk namijin da yazo miki da soyayyah ta gaskiya, matukar dai yana da Sana'ar da zai iya rike ki (samar miki ci da sha, suttura da muhalli), to zaifi kyau ki mayar da hankali akan dabi'unsa.
Akwai mata irin ki dayawa ko wanda suka fi ki cikin wannan duniyar masu dogon burin zaman jiran zuwan miji mai kudi. Wasu na can sun bar gidan iyayen su zuwa bariki, duk a sakamakon dorawa kai dogon buri, wasu talauci da kaskanci ya karu, wasu na shan bakar wahala a barikin, wasu sun mutu a barikin ba tare da samun cimma nasarar auren mai kudin ba, kuma sun tafi lahira ba tare da guzuri ba, dukan yau daban na gobe daban agun mala'ikun Allah.
Wai shin me kike takama dashi na burin sai kin auri mai kudi?
Kyau...?
Surar jiki...?
Iya wanka na jan hankalin maza...?
Iya tafiya...?
Iya soyayyah...?
Tsayinki ko gajartarki...?
To akwai dubun ki shimfide a kwaryar bariki, rayuwa cikin wahala, kaskanci da rashin daraja. Tun ma fa a duniya Kenan.
Mafita daya, kawai ki mayar da hankali akan Wanda yazo neman auren ki da gaske, don baki iya canza kaddarar ki, ba'a yi wa Allah wayo, idan kikayi hakuri da wanda Allah ya baki ta yuwu ke ko babu yin arziki cikin kaddarar rayuwar ki, Allah yaji tausayin ki ya azurta Wanda kike tare dashi yau koh gobe sai ki ci arzikin ta silarsa.
Da fatan yan matan dake dako da jiran sai mai kudi ya fito za su yi aure sun ji wannnan fadakarwar a takaice, gyara kayan ka dai baya taba zama sauke mu raba.
Allah yshiryemu baki daya Allah yasa mudace Ameen summa Ameen.