Yadda Ɗan fashi ya sace wayar ɗan sanda akan hanyar kai shi shalkwatar ƴansanda |
Godwin Emmanuel, dan shekara 23 da ake zargi da yin fashi da makami, ya amince da satar wayar dan sanda a cikin motar sintiri yayin da ake kai shi zuwa shelkwatar rundunar yansanda ta jihar Osun.
An kama Emmanuel ne tare da wasu ƴan fashi biyu, Olajide Kareem mai shekaru 28 da Mike Emmanuel mai shekaru 33, wadanda ake zargi da yi wa mazauna yankin fashi da makami tare da yin lalata da wata mata mai shekaru 65 a hanyar Ilesa zuwa Osu a jihar Osun.
Da ya ke gabatar da wadanda ake zargin a ranar Juma’a, Kakakin Rundunar ƴansandan Jihar Osun, Yemisi Opalola ya bayyana cewa, “’yan bindigar uku sun yi wa masu ababen hawa da fasinjoji fashin kayayyakinsu inda har su ka harbi wani direban bas a kafarsa amma daga bisani aka garzaya da shi asibitin Seventh-day Adventist Hospital da ke Ile-Ife inda ya ke samun kulawa.
“Saboda haka, an kama Olajide a cikin daji, kuma ya amsa cewa shi mamba ne na wasu gungun ‘yan fashi da makami guda biyar da suka fito daga yankin Ikorodu a jihar Legas domin aikata ayyukan su a jihar Osun. An kuma kama sauran biyun da ake zargi.”
Da ya ke magana da manema labarai, Godwin ya ce: “An kama ni ne da laifin fashi da makami. Lokacin da aka kai ni ofishin ‘yan sanda da ke Osogbo, a cikin motar ‘yan sandan da aka kai ni, na saci waya. Ban san cewa wayar ɗansanda ce ba.
"Dan Allah ku yi hakuri, ba zan sake ba," in ji shi.
“Na gaya wa ‘yan sanda kada su yi fushi da ni. Ban san lokacin da na yi haka ba. Na shigar da wayar cikin dakin 'yan sanda ba tare da sun sani ba. Na cire katin SIM, ina so in yi amfani da wayar don kiran mutanena saboda ba su san an kama ni da fashi da makami ba.
Rahoto daga Shafin Daily Nigerian Hausa