Yadda Ƴanbindiga suka cinna wa gonaki wuta a jihar Zamfara |
Wasu da ake zargin ƴanbindiga ne sun cinna wa gonakin manoma da dama wuta tare da yin garkuwa da mutane da dama a wasu ƙauyukan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya
Shafin Bbc Hausa ya rawaito cewa, Maharan sun fara kai harin ne a garin Farin Ruwa da ke ƙaramar hukumar Maru da ke a jihar ta Zamfara, inda suka kone gonakin manoma.
Sun kuma kai irin wannan harin a ƙayukan Wanke da kuma Zargada inda suka ƙone amfanin gona.
Mazauna yankunan da ke iyaka da jihar Kebbi, sun ce ƴanbindigar sun sa sun tafka gagarumar hasarar amfanin gonar da suka noma da ya hada da masara da auduga, da wake da sauran su.
Maharan sun zo ne gungu-gungu tare da cinna wa gonakin masara da wake da dawa wuta, abin da kuma ya haifar da hasara mai ɗimbin yawa.
Sun kuma yi awon gaba da dimbin mutane inda suka ƙona gonaki da dama, kamar yadda wasu daga cikin manoman da suka tafka asarar suka shaida wa BBC.
"Muna cikin ƙunci da wahala, kodayaushe idan ba a kai farmaki ba to za a kashe, akwai matsala."
Rahotani na cewa garuruwan Wanke da Zargada da Dan Godabe na daga cikin wadanda maharan suka addaba.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce matakin da ‘yan bindigar suka dauka na kone gonaki da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, ya sa suna ganin kansu tamkar ba ƴan Najeriya ba.
Ya kuma yi zargin an kyale maharan na cin karensu babu babbaka, kuma babu abin da za su yi face zura ido ga kangin bautar da maharan suka saka su.
"Mutum ma bai sani ba sai ya je gonarsa ya iske ta bushe, sai mutum ya iske bala'in da ya iske sai dai kawai ya yi Kalmar Shahada,"
Sun kuma yi garkuwa da mutum bakwai bayan sun ƙona mana gonaki," in ji wani mazauni yankin.
A ƴan kwanakin nan dai ‘yan bindiga sun fito da wani sabon salon cinna wa amfanin gonar manoma wuta a yankunan arewa maso yammacin Najeriya, da ya hada da dawa da masara da shinkafa da waken suya da sauran su.
Maharan kuma a wasu yankunan kan hana yin noma da kakaba wa manoman haraji tare da yin garkuwa da manoman.
Ko a kwanan nan wasu mahara masu dauke da muggan makamai sun yi irin haka a Birnin Gwarin jihar Kaduna, inda suka kona amfanin gonar da ba a kai ga girbewa ba, da aka ƙiyasta cewa kudinsa ya kai na miliyoyin naira.
Wannan kuma wani mataki ne da zai ƙara jefa yankin cikin barazanar ƙarancin abinci.
Duk da dai ikirarin hukumomi na yaƙar ƴanbindiga a yankin arewa maso yammaci amma kusan a kullum sai an kai hari musamman a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kaduna.