Tarihin Fitattun Malami Ibn Ishaq da ya fara rubuta Tarihin Annabi muhammad (SAW)
![]() |
Tarihin Fitattun Malami Ibn Ishaq da ya fara rubuta Tarihin Annabi muhammad (SAW) |
Ibn Ishaq malamin da ya fara rubuta Tarihin Annabi muhammad (SAW) a Duniya.
Muḥammad bn Ishaq bn Yasar bn Khiyar; bisa ga wasu bayanai, ibn Khabbār, ko Kuman, ko Kutan, da Larabci: محمد بن إسحاق بن يسار بن خيار, ko kuma kawai ibn Ishaq, ابن إسحاق, ma'ana "Dan Ishak" (ya rasu 767) Balarabe ne kuma, Ibn Ishaq ya tattara hadisai na baka masu muhimmanci game tarihin Annabi Muhammad (SAWW). Shi ba masanin lissafi ba ne amma ya horar da likitanci kuma ya ba da gudummawarsa ga aikin.
An haife shi a Madina kimanin shekara ta 85 bayan hijira. Kuma ya rayu a birnin Madina. Yana da sha'awar ya rubuta komai na tarihin rayuwar Annabi (SAWW). Yana zuwa wajen mutanen Madina. Sai ya tambaye su, me kuka ji daga wajen iyayenku game da Annabi? Da Wadanda suka rayu da Annabi bani cikakken bayani. Har ma yakan je garuruwa daban-daban don yin hira da mutanen da suka hadu da Annabi (SAWW) ko kuma iyayensu suka gana da Annabi don sanin rayuwar Annabi (SAW). Kuma ya hada wani littafi wanda ya kai kusan mujalladi 15 a lokacin. Wannan, a lokacin, ƙoƙari ne mai girman gaske. Don haka, Ibn Ish-aq shi ne farkon wanda ya tattara cikakken Sirah da tarihin rayuwar Annabi (SAWW).
Sai ayyukan da Ibn Ish-aq, ya rubuta ya bata saboda karancin takardun rubutu a wancan lokacin talakawa basa iya samun su. Ibnu Ishaq Ya rasu a shekara ta 150 bayan Hijira. An haife shi a shekara ta 85. To, an haife shi kimanin shekaru tamanin bayan wafatin Annabi (SAWW). Ya rayu kimanin shekaru 70 shekara ta 150 bayan Hijira.
Wani mutum mai suna Ibn Hisham, shahararren masanin tarihi ne. Abin da ya yi sai ya dauki littafin Sirah na Ibn Ish-aq ya takaita shi. Don haka Sirah ta Ibn Ish-aq da muke da ita a yau ba ita ce asalin Sirar da ya tattara ba. Juzu'i na 10 zuwa 15, ya ɓace a tarihi. Me ya tsira a yau? Aikin Ibn Hisham. Ibn Hisham ya dauki wannan katon littafi, sai ya ga girmansa ya yi yawa, amma cike yake da cikakkun bayanai. Ya takaita mana shi, ya goge bayanai da yawa. Ya yi wasu kari
Leave Comments
Post a Comment