Al-Qurtubi |
Al-Qurtubi.
Imam Abu 'Abdullah Al-Kurtubi ko Abu' Abdullah Muhammad ibn Ahmad ibn Abu Bakr al-Ansari al-Qurtubi (Larabci: أبو عبدالله القرطبي) (d. 1272) malamin fiqhu ne na kasar Andalus, (Spain ta Yau) malamin Musulunci kuma muhaddith. Manyan malaman Cordoba na Spain ne suka koyar da shi kuma ya shahara da tafsirin Alqur'ani mai suna Tafsirin al-Kurtubi.
An haife shi a Córdoba, Al-Andalus a karni na 13. Mahaifinsa manomi ne kuma ya mutu yayin harin Sifaniyawa a 1230. A lokacin ƙuruciyarsa, ya ba da gudummawa ga danginsa ta hanyar ɗaukar yumɓu don Ginin tukwane.
Ya kammala karatunsa a Cordoba, ya yi karatu daga mashahuran malamai irinsu ibn Ebu Hucce, da Abdurrahman ibn Ahmet Al-Ashari. Bayan kama Cordoba a 1236 da sarki Ferdinand III na Castile Yayi, ya Bar Cordoba Ya tafi Alexandria A Kasar Masar in da ya karanci hadisi da tafsiri. Daga nan ya wuce zuwa Alkahira ya zauna a Munya Abi'l-Khusavb, in da ya yi sauran rayuwarsa. An san shi da tawali'u da salon rayuwarsa ta kaskantar da kai. Ya Rasu A Ranar 29 Ga Watan Afrilu 1273. an binne shi a Munya Abi'l-Khusavb, Masar a an kai kabarinsa zuwa wani masallaci in da aka gina kabari da sunansa a shekarar 1971, har yanzu a bude yake don ziyarta.
Ya kasance gwani sosai wajen sharhi, labari, karatu da shari’a; a bayyane yake a cikin rubuce -rubucen sa, da kuma zurfin ilimin sa Da ya samu karbuwa daga masana da yawa. A cikin ayyukansa, Qurtubi ya kare ra’ayin Ahlus -Sunnah tare da sukar Mu’utazilah.
Ga Abinda Masanin hadisi Dhahabi ya ce game da shi, ".. ya kasance limami masani a fannonin ilimi da yawa, tekun ilmi wanda ayyukansa ke shaida dukiyar iliminsa, da faɗin hikimarsa da ƙimarsa mafi girma."
Ayyuka
1, Tafsirin al-Kurtubi: mafi mahimmanci kuma shaharar ayyukansa, wannan sharhin juzu'i na 20 Sau da yawa ana kiransa al-Jamī 'li-'Aḥkām, ma'ana "Dukkan Hukunci." Sabanin abin da wannan sunan ke nufi, sharhin bai takaita da ayoyin da ke magana kan lamuran shari'a ba.