Tarihin Fitattun Malamai Ibn Rajab |
Abd al-Rahman bn Ahmad bn Rajab, wanda aka fi sani da Ibn Rajab, (wanda shi ne laƙabi da ya gada daga kakansa da aka haifa a watan Rajab), muhaddi ne, malami, kuma masanin fikihu.
Shi ne farkon marubucin Fathul Bari.
Imam Abd Al-Rahman bn Ahmad bn Rajab an fi saninsa da Ibn Rajab Al-Hanbali. Kuma an sanshi da suna Zainuddin. An haife shi a Bagadaza a shekara ta 736 bayan hijira, daidai da shekara ta 1337 miladiyya cikin dangin malamai. Shi kuwa mahaifinsa an haife shi ne a Bagadaza a shekara ta 706 bayan hijira, inda ya girma kuma ya yi karatu a wajen malamai da dama. Sannan ya yi tafiya tare da iyalansa zuwa Dimashku a lokacin da dansa, Ibn Rajab, yana da shekara biyar kacal. A Damascus mahaifinsa ya ci gaba da karatunsa a karkashin mashahuran malamai na lokacin, sannan ya yi tafiya zuwa Kudus, sannan ya koma Bagadaza, daga nan kuma ya tafi Makkah don aikin hajji a shekara ta 749. A lokacin a Makka mahaifin nasa ya shirya cewa dansa Abd Al-Rahman bn Rajab, zai yi nazarin Hadisan da Bukhari ya ruwaito a ƙarƙashin wani sanannen malami. Daga nan sai ya tafi Masar kafin ya koma Dimashƙu, inda ya ke da da'irar koyarwa. Ana yabonsa saboda tsoron Allah, kuma wasu manyan malamai da dama sun yi karatu a karkashinsa.
Ibn Rajab An haife shi a cikin irin wannan yanayi na ilimi, Ibn Rajab ya nuna kokari tun yana karami. Lallai an ba shi damar halartar wajen manyan malamai tun yana dan shekara uku ko hudu kacal. Ya bayar da labarin cewa ya ziyarci malamai a karkashin kakansa tun yana da shekaru uku da hudu da biyar. Ya kuma ambaci cewa ya karanta wasu littafai a wajen wasu malamai yana dan shekara biyar. Abin da ya fi wannan shi ne, tun yana karami ya karbi takaddun shaida a wurinsu. Duk wannan yana nuna cewa Allah ya ba shi basira mai kaifi kuma Allah ya nufeshi shi da son ilmantarwa.
Ibn Rajab yayi tafiye-tafiye don karatu tun yana karami, wanda mahaifinsa ya kwadaitar ta wajen bai wa ‘ya’yansa ilimi mafi inganci.