Tarihin Annabi Muhammadu (S.A.W) Da Aurensa Da Nana Khadijatul Kubra

Tarihin Annabi Muhammadu (S.A.W) Da Aurensa Da Nana Khadijatul Kubra
Tarihin Annabi Muhammadu (S.A.W) Da Aurensa Da Nana Khadijatul Kubra 


A lokacin da ya cika shekaru ashirin da biyar da haihuwa sai ya tafi kasar Sham don gudanar da kasuwanci da wannan dukiya da Khadija bint Khuwailid (r.a) ta ba shi, inda kamar yadda muka bayyana a baya aka samu riba mai girman gaske da ba a taba samun irinta, hakan kuwa saboda albarkar da ke tattare da Annabin ne da kuma irin gaskiya da rikon amanarsa. Wadannan abubuwa dai sun faranta wa Khadijah rai kwarai da gaske da kuma kaunar Annabin.


Khadija dai ta kasance daga zababbun matan Kuraishawa kuma ta fi su kudi da kyau. An haife ta ne a garin Makka kuma a can ta girma, tun a lokacin jahiliyya ana kiranta da "Tahira" (tsarkakakkiya), saboda irin kyawawan halaye da take da su a tsakankanin matayen Kuraishawa.


A lokacin da ta ba wa Manzon Allah (s) dukiyarta don kula mata da su wajen kasuwanci, Khadijah ta hada shi da wani amintaccen yaronta mai suna Maisara. Irin kyawawan halayen Manzon Allah (s.a.w) dai sun yi tasiri wa Maisara, don haka sai ya tafi wajen Khadiza yana gaya mata irin dabi'un Muhammad (s.a.w) da ya gani, wannan ya sa son Manzo ya shiga zuciyarta, sai ta bukace shi da ya aureta, ya zama mijinta, alhali kuwa ta ki amincewa da manyan Kuraishawa wadanda suka zo neman auren nata.


Manzo (s.a.w) dai ya amince da wannan bukata ta Khadijah, inda ya aureta, inda suka tabbatar da mafi kyaun kusanci da ake iya mafarki, wanda ya kyautatu da kauna, alkawari da tausayin juna; suka shata mafi kyawun sura na rayuwar auratayya mai nasara.


Bari mu ji wata hikaya daga Ammar bn Yasir wanda ya kasance abokin Annabi ne tun suna yara kan yadda aure nasu ya kasance da kuma yadda aka daura shi. Ga abin da Ammar din ya ke cewa:


"Ni nafi kowa sanin auren Manzon Allah (s.a.w) da Khadijah bint Khuwailid; don na kasance abokin Ma'aiki (s.a.w). Wata rana muna tafiya tare da Manzon Allah (s) tsakanin Safa da Marwa sai ga Khadijah bint Khuwailid tare da 'yar'uwarta Hala. Lokacin da suka ga Manzon Allah (s) sai Hala ta ja ni gefe ta ce min: 'Ya Ammar! Abokinka ba shi bukatuwa (da auren) Khadijah?


Sai na ce: 'Wallahi ban sani ba. Sai na koma na gaya masa.


Sai ya ce min: "Koma ka sa mana lokacin da za mu je mu gana da ita....sai kuwa na koma na aikata hakan (wato muka sa rana).


Da ranar ta zo.....sai Manzon Allah (s.a.w) ya zo da baffanninsa karkashin jagorancin Abu Talib, inda ya karbi aurenta a hannun baffanta Amru bn Asad, kasantuwan mahaifinta, Khuwailid bn Asad ya rasu.


Bayan gama bukuwan aure, sai Manzon Allah (s) ya koma gidan Khadijah da zama, wannan gida da ke da dimbin tarihi wajen ci gabantar da musulunci da kuma taimakon marasa galihu.


A yayin zamansu dai, Khadijah ta kasance mace mai tsananin biyayya ga mijinta da kuma taimaka masa a dukkan bangarorin rayuwarsa, kamar yadda shi ma ya kasance hakan tare da ita. A lokacin da aka aiko shi a matsayin annabi, ita ce mace ta farko da ta fara imani da shi, ta karbi wannan kira nasa, ta ba da dukkan abin da ta mallaka don Allah da kuma ci gabantar da wannan addini.


Babu makawa, dole ne Manzon Allah (s) ya saka mata saboda irin wannan hidima da ta yi masa da kuma addinin Allah, don haka ya kasance mai tsananin sonta, girmama ta lokacin tana raye da ma bayan rasuwarta (a.s), saboda matsayin da take da shi a cikin zuciyarsa. Irin wannan kulawa da matsayi na Khadijah dai ya sa Annabi (s) bai auri wata mace a lokacin tana raye ba, ko da bayan rasuwarta lokacin da ya yi aure ya kan yawan tunawa da ita, har ya kan ce ita ce matan da ya fi so cikin dukkan matansa. A'a ya ya kuwa ba zai fadi haka ba, alhali kuwa ita ce ta tsaya kyam tare da shi a lokacin yunwa, talauci da wahalhalu wadanda mushirikan Makka suka dora masa, kuma ga ta ita ce uwar dukkan 'ya'yansa, in ban da Ibrahim.


An ruwaito cewa, bayan rasuwarta, a duk lokacin da ya yanka wani abin yanka, ya kan dauki wani bangare na naman ya ce: "Ku aika wannan wa kawayen Khadijah'. An ce wata rana A'isha, matar Manzon Allah, ta tambaye shi me yasa yake haka: sai ya ce mata: "Saboda ina sonta".


Haka nan ma an ruwaito cewa wata mace ta zo wajen Manzon Allah (s), a lokacin yana dakin A'isha. Nan take ya tashi ya karbe ta hannu bibbiyu ya gaggauta biya mata bukatan da ta zo nema. Wannan lamari ya ba wa A'isha mamaki, sai ta tambaye shi dalilin hakan, sai ya ce mata: "Ta kasance tana zuwa gurinmu lokacin rayuwar Khadijah".


Har ila yau kuma an ruwaito A'ishan dai tana cewa: 'Wata rana Manzon Allah (s) zai fita daga gida, sai ya tuna da Khadijah, ya fadi wasu kalmomi na girmamawa gare ta. To amma sai na gagara rike kai na sai na ce masa; 'Ita dai ba wani abu ba ne face tsohuwar mace, kuma a halin yanzu Allah ya musanya maka wadanda suka fi ta'. Nan take Manzon Allah (s) ya mayar mata da martani, cikin fushi yana cewa: "Lallai ba haka ba ne...lalle ban samu wadanda suka fi ta ba. Don kuwa ita ce ta yarda da annabcina a lokacin da kowa ya kyale ni. Ta ba ni dukkan dukiyarta a lokaci mafi tsanani (na bukatuwa da su). Kuma Allah Ya ba ni zuriya ta hannunta, alhali kuwa ya haramta min daga wasunta".


Khadijah ta ci gaba da taimaka wa Manzon Allah, har lokacin da Allah Ya karbi ranta a shekara ta goma bayan wahayi, wannan rasuwa nata dai ya kasance babban abin bakin ciki ga Manzo, bugu da kari kuma kan rasuwar Baffansa kana kuma mai kare shi Abu Talib (a.s), don haka ma ya kira wannan shekara ta sunan Shekarar Bakin Ciki.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post