Shin NLC na iya tilasta wa gwamnoni biyan albashi mafi ƙanƙanta?

Shin NLC na iya tilasta wa gwamnoni biyan albashi mafi ƙanƙanta?
Nigeria NLC 


Ƙungiyar ƙwadago NLC ta Najeriya ta umarci ma'aikata a jihohin da gwamnatocinsu ba su aiwatar da sabon tsarin albashi mafi ƙanƙanta ba da su shiryawa tsunduma yajin aiki nan da ranar 1 ga watan Disamba.


Ƙungiyar ƙwadagon ta bayyana cewa jan ƙafar da jahohin ke ci gaba da yi wajen aiwatar da sabon tsarin albashin, wani nau’in cin zarafi ne da tauye hakki.


Shafin BBC Hausa ya rawaito cewa, Kungiyar kwadagon ta bayyana umurnin a cikin wata takardar bayan taro da shugabanta, Mista Joe Ajaero ya fitar, lokacin da suka kammala taron majalisar zartarwa ta ƙungiyar a birnin Fatakwal.


NLC ta nuna da damuwa da rashin amincewa da jan kafar da wasu jihohin a Najeriya ke ci gaba da yi wajen aiwatar da tsarin albashin mafi karanci na 2024, kuma a cewar ta abu ne da ya saba ma doka, tare da tauye hakkin ma’aikata musammam a wannan yanayi na matsin rayuwa.


Wani bayani da ofishin tattara bayanai game da basussuka na Najeriya ya fitar ya nuna cewa bashin da ake bin jahohi 36 na kasar ya kai naira tiriliyan goma sha daya, inda aka samu karin kashi 14 daga kashi goma da ake da shi a watan Disamban 2023 ta gabata, duk kuwa da kudaden kwamitin rabon tattalin arziki na kasa ke ware musu a duk wata.


Kwamared Ayuba Waba tsohon shugaban kungiyar kwadagon ta NLC , wanda kuma yana daya daga cikin jagororinta, ya ce " Sanin kowa ne cewa tun ranar da shugaban ƙasa ya rattaba hannu kan mafi ƙanƙatar albashi na 70,000 ya zama doka a Najeriya."


Kwamred Waba ya ce jihohi da yawa sun aiwatar da wannan tsari, sai dai akwai wasu jihohi da ba su da niyyar aiwatarwa,"Amman wadanda an saba ba su biya kuma babu niyyar biya, su ne wannan mataki zai shafa, domin a karɓo wa ma'aikata haƙƙinsu."


Ƙungiyar ta NLC ta lashi takobin maganin abin da ta kira rashin tausayi na gwamnonin wasu jihohi a ƙasar na ƙin amincewa da sabon tsarin albashin, abin da ya sa ta yanke shawarar tsunduma yajin aiki daga ranar daya ga Disamba.


A watan Yulin shekarar 2024 dai ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da albashi mafi kankanta na naira dubu saba’in.


Duk da wasu jahojin sun ki soma biya amma a makon farko na wannan watan nan na Nuwamba fiye da jahohi 20 suka bayyana amincewa da fara biyan sabon tsarin albashin wadanda suka hada da Kebbi da Borno da Adamawa da Legas, da Osun da Ogun da Ondo da Ribas da Kogi da sauransu.


Abin zuba ido a gani yanzu shine ko saura jihohin da basu ayyana fara biyan Sabon karin albashi za su fara a kusa ne ko kuma sai tsawon wani lokacin?


Rahoto daga Shafin BBC Hausa


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post