Shin Gaskiya ne Dankalin Hausa na da alaka da jawo ciwon basir?

Shin Gaskiya ne Dankalin Hausa na da alaka da jawo ciwon basir?
Dankalin Hausa 


Mutane da yawa kance Idan sun ci Dankalin hausa yana sakawa ko tayar musu da Basir. To shin da gaske Dankalin hausa na da alaqa da Basir?


Abunda ya kamata a sani shine, Dankalin hausa na dauke da sinadarin Fiber wanda yake taimakawa wurin lafiyar hanji da motsawar sa da saukaka fitar bayan gida.


A bayanin baya kuma Idan ba'a manta ba, cikin abubuwan da kan kawo Basir harda yawan Zawayi.


Dankalin hausa baya saka Zawayi amma yana saka laushin bahaya, idan an tashi cinsa kuma irin hadin da ake masa yana taimakawa wurin sakewar ciki.


Misali wasu Idan sun tashi cinsa sai sun kwaba yaji da mai da za'a ringa dangwalar sa anaci har a gama. Sai kaga kafin mutum ya gama cin Dankalin ya ci yaji da yawa ga kuma maiko.


Dama kuma yaji na daga cikin abunda ke saurin rude ciki a tsure da gudawa, gashi kuma an hada da Dankalin hausa wanda shi kuma yana taimakawa wurin saka laushin bahaya.


Cikin lokaci kadan mutum zai iya fara Zawo wanda yana taimakawa wurin saurin kumbura jijiyoyin hanyar fitar bayan gida (Anus).


Wannan dalilin ke sawa ake cewa yana saka Basir. Dankalin Hausa Baya tayarwa ko saka Basir, yanayin yadda aka sarrafashi da kuma tsaftar kayan da akayi amfani dasu lokacin sarrafashi ne kan haifar da Zawayin da har jijiyoyin hanyar fitar bayan gida zasu kumbura wato Basir kenan!


Amb(Nr)Sumayya Ibrahim Sa'ad 

RN,RM,PND 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post