Sakamakon luguden wuta daga sojoji yasa yan ta'addan Lakurawa tserewa daga jihohin Arewa - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Sakamakon luguden wuta daga sojoji yasa yan ta'addan Lakurawa tserewa daga jihohin Arewa

Sakamakon luguden wuta daga sojoji yasa yan ta'addan Lakurawa tserewa daga jihohin Arewa
Lakurawa

Lakurawa sun fara tserewa daga jihohin Kebbi da Sakkwato sakamakon luguden wuta daga sojoji 


Mambobin kungiyar Æ´an ta'adda ta Lakurawa sun fara tserewa yayin da sojoji suka kara kaimi wajen kai hare-haren kasa da na sama a sansanonin kungiyar a fadin jihohin Kebbi da Sokoto.


Daily Trust ta rawaito cewa biyo bayan harin da kungiyar Lakurawa ta kai a garin Mera a karamar hukumar Augie ta jihar Kebbi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 17, shelkwatar rundunar soji ta tura wasu dakarun sojoji zuwa yankin.


A lokacin da suka isa Birnin Kebbi, dakarun, kamar yadda Abdullahi Idris Zuru, mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai na gwamnan Kebbi ya bayyana, sun gana da mataimakin gwamna Abubakar Umar Tafida a Ofishin Majalisar Zartarwa kafin su wuce zuwa Mera.


Zuru ya ce dakarun sun samu nasarar korar 'yan bindigan tare da kwato shanun sata da suka bari a lokacin da 'yan ta'addan suka tsere.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel