Naƙasu da koma bayan da ake samu a dalilin siyan ƙuri’u da 'yan siyasa ke yi – Abdulsalami Abubakar

Naƙasu da koma bayan da ake samu a dalilin siyan ƙuri’u da 'yan siyasa ke yi – Abdulsalami Abubakar
 Abdulsalami Abubakar 

Abdulsalami Abubakar, wanda shi ne Shugaban Kwamitin zaman lafiya na ƙasa (NPC), ya bayyana hakan a lokacin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaɓen gwamnan jihar Ondo da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba.


Aminiya ta ruwaito cewa, An gudanar da taron yarjejeniyar ne a garin Akure, babban birnin jihar a ranar Juma’a. Wanda ‘yan takarar jam’iyyun siyasa 17 da suka shiga zaɓen sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.


Abdulsalami ya buƙaci ‘yan takarar gwamna da su amince da sakamakon zaɓen matuƙar an yi zaɓe cikin gaskiya da aminci.


Ya ce duk ‘yan takarar da ke ganin bai gamsu da sakamakon zaɓen ba zai iya neman halaltacciyar hanya ta zaman lafiya don gabatar da ita kan wata damuwa da ka iya tasowa bayan zaɓen.


“Ina kira ga duk ‘yan siyasar da za su rattaɓa hannu kan yarjejeniyar da su bai wa kansu da jam’iyyunsu cikakku kan yarjejeniyar da su ƙaurace wa tashe-tashen hankula da tsoratarwa, su kuma tuna cewa a matsayinku na ‘yan siyasa, dole ne ku nuna halin kishin ƙasa domin wannan shi ne  kyakkyawan hali na shugabanci,” in ji shi.


“Ya zama haƙƙi na ‘yan Nijeriya su zaɓi shugabanninsu ba tare da nuna son kai ba. ’Yan siyasa su daina barazana ta cinikin ƙuri’u.”


A yayin da yake yaba wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) bisa ayyukan da ta gudanar ya zuwa yanzu, Abdulsalami ya roƙi hukumar zaɓe da ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na tabbatar da cewa masu kaɗa ƙuri’a sun gudanar da zaɓensu cikin lumana. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post