ciwon hanta |
Ga sahihin maganin ciwon hanta da ake hadawa da albasa
Duk wanda ya Karanta wannan rubutun yai kokari wajen yin share, Allah ya hadamu a ladan gabaki daya amin.
Duk wanda yake fama da ciwon hanta ya gwada wannan maganin da ikon Allah za'a dace a samu waraka cikin karamin lokaci.
Ku samu albasa wato onion guda shida 6 manya sannan a yayyanka su kamar za'ayi miya, Sai a samu ruwa kamar galon daya, daidai da litre 5 sai a raba ruwan gida biyu, sai ka dauki rabin ruwan wato half galon sai a dafa albasar da rabin ruwan.
Bayan an gama dafa albasar, sai a tace albasar sannan a zubar da tukar albasar, sannan sai a dauko rabin ruwan da aka ware sai a hada shi da abin ruwan da aka dafa albasar kaga ya dawo galon guda kenan,
Saanan sai a samu zuma mai kyau, sai a samu karamin kofi irin na silver ko kuma karamin kofin roba. Za'a rinka cika karamin Kofi, sai ka dibi zuma kamar cokali uku ka saka a cikin kofin kana sha sau uku a rana har sai ruwan ya kare da zuman.
Bayan ka gama kaje asibiti ka yi gwajin ciwon hanta, insha Allah za'a samu babu ciwon gaba daya da yadda Allah, Allah yasa a dace.
Daga karshe ina rokon duk wanda suka yi amfani da wannan maganin ciwon hanta su yi mana addu'a, Allah ya kara mana lafiya da sauran al'umma marasa lafiya, da zaman lafiya a kasarmu baki daya amin.
Don Girman Allah idan ka Karanta ka yada domin Alummar Annabi su amfana.
Daga : Ummu Hamid