Masu duba jarrabawar NECO na shirin yin zanga-zanga bisa zargin danne musu haƙƙoƙi |
Masu duba jarrabawar da hukumar shirya jarabawa ta kasa, NECO, ta shirya ta 2024, sun yi barazanar fara zanga-zanga a fadin kasar, kan rashin biyansu hakkokinsu bayan kammala aikin.
Jaridar PUNCH ta samu labarin cewa masu jarrabawar sun fara hada kan takwarorinsu a fadin jihohin kasar domin gudanar da zanga-zangar.
Wasikar da suka rubuta wa babban magatakardar NECO a hedikwata ta kasa da ke Minna, kuma aka raba wa masu duba jarrabawar NECO a jihar Plateau, ta tabbatar da shirin na yin zanga-zangar.
Wasikar mai dauke da kwanan watan 8 ga watan Nuwamba, 2024, kuma aka aikewa daukacin shugabannin kungiyar da mataimakan su a fadin tarayya, wacce wakilin jaridar Punch a Jos ya samu a yau Lahadi ta nuna cewa sun nuna bakin ranau akan kin biyan su hakkokin su.
“A matsayinmu na masu duba jarrabawa, waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da gudanar da jarabawar mun ga cewa ba a ganin sadaukar da kai da jajircewarmu wajen gudanar da ayyukanmu, kuma bai kamata a fuskanci irin wannan sakaci da rashin kula da jin walwalar mu ba, musamman a wannan lokaci na matsalolin tattalin arziki.
“Saboda haka, muna ba NECO wa’adin mako biyu don warware matsalolin da suka shafi biyan mu hakkokin mu. Idan har ba a warware wannan batu cikin wa'adin da aka gindaya ba, masu duba jarrabawar ba su da wani zabi illa fara zanga-zanga a fadin kasar ta hanyar hadin gwiwa da mambobin mu a fadin jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya (Abuja).