Manyan hafsoshin soji 6 ne suka rasa rayukansu a hannuna yan ta'adda
![]() |
Manyan hafsoshin soji 6 ne suka rasa rayukansu a hannuna yan ta'adda |
Rahotanni sun bayyana cewar aÆ™alla manyan hafsoshin soji shida na Jamhuriyar Chadi sun rasa rayukansu, tare da jikkatar wasu da dama a wani harin kwanton É“auna da ’yan ta’addar Boko Haram suka kai wa sojojin Æ™asar a gaÉ“ar Tafkin Chadi.
Shafin Aminiya ya rawaito cewa, Ƙwararren mai sharhi kan yaÆ™i da tayar da Æ™ayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ’yan ta’addan na Boko Haram sun aiwatar da wannan hari ne a ranar Juma’a, 8 ga watan Nuwamba.
Makama ya ce har na zuwa jim kaÉ—an bayan Shugaban Kasa Mahamat Idriss Deby ya tashi daga yankin domin komawa babban birnin kasar, Ndjamena.
Daga cikin waÉ—anda suka rasu akwai manyan hafsoshin kasar da suka haÉ—a da Janar Youssouf Abdoulaye Kari, Janar Adoum Issa, Kanar Lony Allatchi, Laftanar Kanar Gorou Wardougou, Adam Nassour Mahamat, da Idrissa Malloum.
Har ila yau harin ya yi sanadin raunata wasu manyan Hafsoshinn sojoji, kamar Janar François Tatiko, Janar Moubarack Formalick, Bokhit Bachar, Laftanar Jean Pierre Medar, da Ibrahim Ali.
Janar Youssouf Abdoulaye Kari, tsohon sojan da ake mutuntawa, kuma tsohon mamba ne na rundunar sojojin Chadi a Mali, na daga cikin waÉ—anda aka kashe, wanda ya bar baya da kura a shugabancin soja.
Kazalika, kakakin rundunar sojin ƙasar Chadi, Janar Issakha Acheikh ya fitar da sanarwa dangane da wannan harin na kwantan ɓauna da aka yi wa sojojin ƙasar amma bai yi wani ƙarin bayani ba.
Zagazola ya ambato Babban Hafsan Sojin Æ™asar yana cewa tuni an yi garambawul ga rundunar OPERATION Haskanite da aka ba da umarnin Æ™addamar da shirin fatattakar ‘yan ta’addar Boko Haram daga Tafkin Chadi, inda har sun yi artabu na farko a ranar, Asabar 09 ga watan Nuwamba, 2024.
Ya yi bayanin cewa, bayan shafe sa’o’i kaÉ—an ana gwabzawa, an kashe ‘yan ta’addan da dama, kuma an ci gaba da kai farmakin yayin da ya Æ™ara da cewa nan gaba za a sanar da Æ™arin bayani.
Leave Comments
Post a Comment