Mafi Yawan Mata Masu Amfani Da “Sha-Ka-Fashe” Ƴan “Lesbian” Ne |
Cikin ikon Allah na samu damar gudanar da wani binciken sirri a matsayi na na Likita, kuma wanda ke wayar da kan al’umma kan harkar lafiya. Na samu zarafin zantawa da mata da dama wanda da yawan su ƴan maɗigo (lesbians) ne kuma daga mabanbantan jahohi na Arewacin Nigeria.
Babban dalilin gudanar da wannan bincike na ƙwaƙƙwafi shi ne, ganin yadda al’umma suka damu da yadda ƴan mata suke yawan amfani da wannan magani na “Sha-ka-fashe”. Haka-zalika, sanin illolin wannan magani da nayi a Likitance ya sa ni dole na tashi tsaye wajan gano bakin zaren. Domin ta haka ne kaɗai zan iya samun damar bada shawarwari da faɗakar da masu amfani da shi domin su daina. Dalili kuwa shi ne idan baka san dalilin yin abu ba to ba za ka iya bada maganin wannan abu ba.
Da farko dai ya zama wajibi na miƙa godiya ta musamman ga dukkan ƴan madigo (lesbians) da suka taimaka suka shiga cikin wannan bincike da nayi ta hanyar amsa tambayoyin da na yi musu da kuma ƙara haɗa ni da suka yi da abokanan su daga shiyya-shiyya. Tabbas su ma waɗanda ba ƴan lesbian ba da suke amfani da wannan magani suma ina miƙa godiya ta gare su domin samun dama da sukai wajan amsa tambayoyin mu.
Babban abun da ya ke sa mata shan maganin “Sha-ka-fashe” shi ne domin kara girman mazaunai (hips), cinyoyi (thighs), da kuma nonuwa (breasts). Kamar yadda na samu bayani, wannan su ne manyan dalilan su. Kuma wannan buri na su ya samo asali ne daga yadda a cikin harkar maɗigo (lesbianism) ake daukar su da muhimmanci domin idan mace a rame take, ba'a fiya sha’awar ta ba. Amma sun tabbatar mun da cewa buƙatuwar hakan yafi yawa wajan waɗanda suke zama kamar mace (feminine role) ba wacce take zama 'namiji' (masculine role) ba.
Sakamakon binciken ya nuna cewa mafi yawan mata suna amfani da kala-kalar magunguna da dama, amma akwai wasun su da suke amfani da “allura” ba magani ba. Dalilin su na amfani da allura shi ne, ba sa iya jimirin haɗiye ƙwaya kullum. Haka-zalika, sun karkata ga amfani da allura ne saboda a tsammanin su, allura na da ƙarancin illoli idan aka kwantanta ta da magani na sha.
Sun tabbatar mun da cewa waɗannan magunguna suna fara nuna tasiri a jikin su cikin wata ɗayan farko da suka fara amfani da su, inda kuma wasu suke cewa sati biyu. Amma dai mafi yawan su wata ɗayan farko suke cewa. Sun tabbatar mun da cewa suna masifar samun cigaba da kuma samun kuɗi a rayuwar su matuƙa sosai a yayin da suka fara samun canjin yanayi. Wannan kuɗi suna samu ne ta wajan yawan abokanai na harkar su ta mu’amalar arziƙi ta maɗigo kamar yadda suka bayyana min.
Amma a inda gizo ke sakar shi ne, mafi yawa daga cikin su sun tabbatar mun da cewa gaskiya sun dan haɗu da wasu ƙalubale da dama yayin da suke shan magungunan wanda suka hadar da matsanancin ciyon kai, rashin bacci, jiri, da yanayin damuwa. Waɗannan alamomin suna samun sune a farkon fara amfani da maganin ne.
Akwai wacce tace min sakamakon shan magani da allurar “Sha-ka-fashe” duk sati sai tayi zazzaɓi kuma taje asibi amma ance mata garkuwar jikin ta tayi rauni saboda amfani da maganin ƙiba. Kuma gaskiya ne haka abun yake ko a likitance tabbas jinsin wadannan magunguna (wanda aka fi sani da ‘steroids’) suna kawo raunin garkuwar jiki!
Babu abin da yafi ɗaure min kai sama da wacce tace min yanzu haka ba ta gani sosai sakamakon amfani da waɗannan magunguna. Kuma gaskiya ne suna kawo lalurar rashin gani. Wata kuma ta samu matsalar taruwar ruwa a jiki (water retention) wanda da gaske waɗannan magunguna suna kawo hakan. Wannan kaɗan daga cikin illolin da wasu suka bayyana min sun samu kenan.
A ƙarshe ina mai cewa wannan bincike da muka yi ba munyi ne domin tozarta wasu ba ko kuma nuna rashin dacewar yadda wasu suke rayuwa ba, face munyi ne domin gano wasu muhimman abubuwa, wanda insha’Allah za mu wallafa wannan bincike a cikin harshen ingilishi tare da saka duk wasu alkaluma da duk ma abun da ba mu saka anan ba. Dalilin yin hakan kuma shine domin mu isar da saƙo gurin mutanen mu na Arewacin Najeriya. Har kullum dai muna cewa “rigafi yafi magani.”
Dr. Khalid Sunusi Kani
Likita Kuma Me Wayar Dakan Al’umma Kan Cututtuka Da Dama.