Celebrities
Jarumar TikTok Asmee Ta Watsar Da Tafiyar Barau Jibrin Ta Koma Kwankwasiyya
Friday, November 8, 2024
0
![]() |
Asmee Wakili |
Jarumar Kannywood kuma Tauraruwar TikTok Asma’u Wakili da aka fi sani da Asmee ta koma tallan Kwankwasiyya kwanaki kadan bayan Sanata Barau Jibrin ya karbe ta a APC.
Wakili dai tana cikin manyan yaran tsohon SA din Gwamnan Kano a Kannywood Sunusi Oscar.
Tana cikin jaruman da hukumar tace fina-finai ta Kano ta hukunta a Gwamnatin Kwankwasiyya bisa zargin yin rashin tarbiyya.
Sai dai a wannan makon an ganta a wajen Sanata Barau Jibrin inda ta bayyana cewa ta yi watsi da Kwankwasiyya.
Sai dai kwatsam Jarumar ta koma tallata Kwankwasiyya a shafinta na TikTok inda ta yi bidiyo da Jar Hula a kanta mai dauke da sakon wakar Dauda Kahutu Rarara inda ya ke cewa ‘Ga shi Jamila ta yi bari…’.
Shin me za ku ce a kai?
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment