Illolin magungunan da mata ke amfani dasu don karin girman nono da mazaunai |
Nasan duk macen dake yin amfani da irin wadannan magungunan taina so ta ƙara girman ababen halittar ta sabida ta burge mai gida ko ta ƙara farin jini wajen samari. Sai dai kin sani cewa akwai magungunan da su ke da illa idan har za ki yi amfani dasu, magunguna kamar su sha ka fashe, muna ta fadakarwa akan illolin shan shi cewa yana iya kawo hawan jini, ciwon suga, ciwon Gaɓɓai, kumburin jiki da matsalar koda.
A dalilin haka sai kika ce ke kin hakura da amfani da sha ka fashe, za ki samu maganin gargajiya wanda yake PURELY NATURAL, watau tsantsan na gargajiya ne. Sai ki ka siyo:
- Zuman ƙara nonuwa da mazaunai
- Garin ƙara ƙiba
- Haɗin ƙara ƙiba da sauran nau'in magunguna.
Mata da yawa suna tambaya na, shin amfani da waɗannan magungunan na da illa ko bashi dashi?
Bincike na sirri ya bayyana mana wani abin tada hankali. Yawanci masu iƙirarin cewa maganin su purely herbal/natural ne ƙarya suke.
Misali:
Wata mata na siyar da:
Garin kunu na gyaɗa da riɗi mai ƙara ciccikowan hips da nonuwa da ni'ima ga mace.
Ashe ba gyaɗa da riɗi kaɗai take sawa a cikin kayan haɗin na ta ba. Tana siyo SHA KA FASHE ta haɗa a ciki takai niƙa. (Kamar yadda za'a gani a hotunan nan).
Yanzu ke da ke kula da lafiyar ki, kike gujewa amfani da sha ka fashe saboda illolin shi amma kike siyan irin Wannan magungunan, ashe an gudu ba'a tsira ba.
Jama'a muyi taka tsantsan da irin magungunan da muke sha, mu tuna wasu fa kuɗin kawai suke so ba ruwansu da lafiyar jama'a.
Sunana Pharm. Musa A Bello, fadakarwa da ilmantar wa game da lafiyar ku shi ne nawa, sai kuyi share da like domin mutanen mu su amfana su kare lafiyar su.