Hanyoyin da ma'aurata za su inaganta mu’amalar Aurensa |
Daga cikin hanyoyin inganta mu'amalar shimfida tsakanin ma'aurata, Yana da kyau abokan zama su san kan su sannan su sani kuma su fahimci abokin zaman su.
Yana da kyau su san abubuwan da abokin zaman su ke so kamar irin wasanni da positions da yake so, yaushe yake so misali na dare ko kafi shayi ne, yaushe ya/ta fi bukata misali kafun period, bayan period, in yana cikin stress, damuwa, kafun yayi tafi, bayan ya dawo, in kuna da matsala, in yana cikin farin ciki, in an shirya bayan saɓani, etc, ko yanayin sha'awar sa wato mai tsanani, karanci ko rashin sha'awane.
Yana da kyau ma'aurata su zama masu furtawa ko nunawa juna abunda suke so, yadda suke so da yaushe su ke so, dan ba yadda za'ayi abokin zama yasan abunda kake so in baka nuna ko sanar masa ba.
Yana da kyau a na samun daidaito tsakanin ma'aurata akan bukatar sha'awar su, misali in daya yafi daya ya dace mai yawan sha'awa ya dan rage na shi, mai karanci ya daga na shi dan asamu balance kuma a gujewa cutar da ɗaya.
Haka kuma ya dace abokan zama su fahimci lokaci da kowani abokin zama ke dauka kafun ya bukata, wani kusan kullum yana/ta bukata, wani yakan dauki kwanaki, wani sati, wani watanni bai bukata ba.
Hakan yasa yake da muhimmanci ko da kai baka da bukata abokin zaman ka zai iya bukata tunda ba lallai lokutan da ku ke dauka na bukatar yi ya zama daya ba.
Ya dace ko ince mafi chanchanta shi ne ma'aurata su kasance su na tambayar abokin zaman su ko ya/ta na da buqata, in bai da bukata kuma kaima baka da buqata shikenan, in kuma yana da baqata ko da kai baka da buqata sai ayi, amma ba dadi kuma bai dace ba daya ya nuna buqatar sa alhali abokin zaman sa yayi watsi da buqatar dan shi bai da buqata.
Kuma dan ka nuna bukata abokin zaman ka ya bada ingantaccen uzuri yana da kyau a kiyaye kar ayi fushi ko aji haushi dan kaima wani lokaci zaka iya samun uzuri da zaka so a ma uzuri.
Haka kuma ke mace in kina da uzurin da zai hana ki bama miji kan ki, yana da matukar kyau da muhimmanci in kika lura mijin ki mai karancin hakuri ne sai ki samar masa da hanyoyi da zaki gamsar dashi, dan wani fada da haushin sa baya tashi sai mace tana al'ada, haka zaita jin haushinta har sai randa tayi resuming duty za a zauna lafiya dashi.
In kuma kika lura da bukatar mijin ki yafi karfin bukatar ki ko yama fi karfin ki bar shi ya karo aure.
Yana kuma da matukar muhimmanci mu sani kuma mu gane barin abokin zama da yunwar sha'awa yana iya jefashi cikin fitina sosai wadda zai iya shafar lafiyar jiki, zuciya da auren ku.
Yana da kyau mu gane dukkan abunda na fada anan yana da alaka da muhimman abu 3 wato :-
1. Sadarwar
2. Fahimta
3. Daidaito
Dole a samu wadannan abubuwa dan samun ingantaccen mu'amala a tsakanin ma'aurata.
✍️ Fatimah Chikaire