Halin da mata kan iya fuskantar kansu a dalilin amfani da maganin Sha Ka Fashe

Halin da mata kan iya fuskantar kansu a dalilin amfani da maganin Sha Ka Fashe

 Illolin amfani da maganin Sha Ka Fashe 


Ku bani aron lokacin ku masu son su yin kiba


Akwai wani kuskure dake cigaba da faruwa tsakanin Mata na shan maganin da suke kira Sha-ka-fashe domin son su yi ƙiba. Wannan magunguna kala biyu da idan kun haɗa kuke kira da sha-ka-fashe tabbas magungunan asibiti ne da aka ware musamman don wasu larurori amma ba don saka ƙiba ba.


Likitoci na amfani dasu ne wajen tackling histamine receptors a kwakwalwa da kuma guda wajen raunana garkuwar jiki da baiwa jiki damar warkewa daga masassara, ko baiwa jiki ikon karɓar baƙon abinda aka dasawa mara lafiy a jiki kamar a masu ciwon ƙoda da akai musu dashe, ko amfani dashi dalilin cuttukan kafofin iska dakan shafi hutu koma cutar cancer.


Shi wannan Maganin yana da illa a sanda kake yi mara lafiya amfani dashi kamar a cutar Cancer ko Ƙanjamau wanda illar shine hura mutum. Wato abinda muke kira da SIDE EFFECTS! yakan haddasa kumburin dukkan sassan jiki ya zamto mutum yai hum yai ƙiba...


Wannan illar tasa itace: Mata ke rubunbu sa har suka halastawa kansu shi a matsayin maganin sanya ƙiba.


A yau zaka samu Mace a bushe, bata da wata cima me kyau ko inganci kurum karau-karau a bushe amma ta samoshi ko kuwa wata ta bata shawarar nemo shi tana ta sha kan zatai ƙiba. Mata sun matukar bude ido dashi ƙauye da birni, har takai ana samun wasu kananun jami'an lafiyar da basu da ilimin magani suma suna rubutawa Mata shi. 


Toh albishirin duk wacce ta ɗau wannan Layin na shan sha ka fashe, ina mai tabbatar miki da ki kwan da shirin zaki haɗu da ciwon sugar (Diabetes mellitus) yes. 


Ko kwanaki nai magana a game da yadda yan Mata 4 tun basu kai ga aure ba suka jawowa kansu DIABETES dalilin shan wannan maganin. Sun zo suna turomin sako suna kuka kan sunje suna fama da wasu matsaloli  an dubasu ance suna da ciwon sugar. 


Ɗaya har tana bayyana min cewa wani Nurse ne ya bata. Wanda Kunga wannan na daga cikin trust, wato yadda tsakanin jami'i lafiya da mara lafiya. Shi sai ya biye wa me take so batare da aiki da ilimi ba, wanda abinda wasu da yawa daga cikin jamian lafiya ke aikata wa kenan.


Alhalin sanda irin wadannan matan a hannu daya kake fada musu gaskiya amma basaji.


Don haka ina kara jaddada miki koda a yanzu kin daina sha kuma bukatarki ta biya ƙibar da kika nema ta samu toh ina me shawartarki da lallai duk bayan wata 4 kike zuwa gwajin sugar. Domin idan matsalar tai KICK-IN ki tare ta da wuri kafin tai miki gagarumar illah. Kin riga kin cutar da jikinki.


Idan kuma kinki, to fa idan kikai wasa ciwon sugar ya shige ki baki fargaba akan kari har saida alamu suka bayyana. To babu makawa akwai yiwuwar zaki mutu bakisan ma waye kanki ba saboda tsananin ciwo.


Babban abin tsoron shine ciwon sugar da masu wannan halayyar kan hadu dashi bama type 2 bane dake jin magani ta baki idan ansha... A'a STEROIDS DIABETES ce me kama da Autoimmune wacce maganin ciwon SUGAR ma nasha bayayi sai dai mutum ya rika yin allurar insulin. Idan bakusan nawa ce allurar insulin ba ku tambaya kusha labari, kuji a sati 1 ta dubu nawa kuke bukata.


Babu wani Medical doctor da zai taɓa bawa Mace shawarar shan wannan maganin don tanason tai kiba, sai dai idan baisan me yake ba. Galibi wannan matsalar kananun ma'aikatan lafiya ke assasata domin 99% basusan ma pharmcodynamic na magunguna ba su dai sunga wani yayi. Don haka ku takawa wannan ɓarnar birki. 


Baya ga ciwon sugar, cutar hawan jini da gudardaji cikin jini (blood clots) duk matsaloli ne daka iya faruwa dalilin hakan wanda bugun zuciya ko strokes na iya kashe mutum farar daya. 


Na faɗa zan kuma maimaitawa; Ba'a taɓa samun ƙiba ta hanyar magani har yau har gobe babu wannan maganin a duniyar likitanci, ƙiba a abinci da kwanciyar hankali take sai kuma gado. Duk maganin da za'a baka inde ba MULTIVITAMIN da zaisa ka kama abinci da kyau ba ko ki bar ta samu. Toh tabbas an shiga kame-kame. Ku dain sawa jikinki unnecessary products. 


Kowa yaiwa kansa fada, idan ma kina sha toh ki watsar dasu tun wuri, idan kuma anki ji toh ba'a ki gani ba. Kai kuma duk wacce tazo da korafin rama ba magani ake tunani ba kokari ma zakai ka gano dalilin ramewar... HIV, Depression, Diabetes, Cancer, Tuberculosis duk na daga cuttukan daka iya sanya rama. Meye amfanin magani idan baka magance tushen matsala ba. 


Da fatan an fadaka daga wannnan sako, sannan da fatan za ku yi kokari yin share domin sauran mata su amfana. 


Ni nayi nan.... 

Daga Ibrahim Y. yusuf


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post