Halaye Dake Iya Lalata Lafiyar Mutum Cikin Shekaru Kaɗan |
Tabbas a wannan zamanin wasu nau'in rashin lafiya sun yawaita ba kamar a baya ba da zai yi wuya ace kasan masu irin matsalar sai dai a baka labari, Misali: Ciwon Koda (Kidney Disease), Ciwon Daji (Cancer), Ciwon Sukari (Diabetes), Cutan Damuwa (Depression) har ma da hawan jini (Hypertension).
Wasu daga cikin wadannan cutukan yanzu sun yawaita, kuma suna kama matasa sosai. Duk da cewa abubuwa da yawa ne ke iya haifar da su (Several Factors), Amma akwai halaye da suka yawaita abin. Kaɗan daga cikin halayen su ne:
1. Yawan Shan Kayan Ƙara Ƙarfi (Energy Drinks): Wani kullum sai ya sha FE@RLÉSS da irinsu guda uku ko fiye da haka. Yanayin yawan sinadarin CAFFEINE dake cikin wannan abin nada ƙarfi, hasali ma shi yasa ake gargadi mai ciki da yara basa sha.
2. Rashin Motsa Jiki: Yanzu muna wani yanayi da mutane sun sangarce, tafiya 'yar kaɗan sai an hau abin hawa (keke napep), mashin ko mota. Wanda hakan yasa ba'a samun mafi ƙarancin motsa jikin da ake bukata. Domin inganta lafiya, musamman lafiyar zuciya da jiki, ana so mutum yayi tafiyar aƙalla minti 30 a rana, jumulla mintuna 150 a sati.
3. Yawan Cin Abinci Zamani (Irin su Cake, Shawarma, Waken Gwangwani, Abincin Gwangwani da sauransu), abinda bature ke ce ma JUNK FOOD: Cin su jefi jefi ba matsala bane, amma mutum ya sa ma kanshi yawan cin su na da matsala domin ba abincin gina jiki bane su. Mutum sai yafi lafiya idan yana cin abincin da aka girka ba wai irin wanda aka sarrafa shi ba kawai.
4. Shaye Shaye: Fara daga shaye shayen lemun kwalba/roba ba bisa ka'ida ba izuwa shaye shayen kayan maye. Wannan halin na cikin abinda ke lalata lafiyar mutum.
5. Yawan Tunani: Muna zamanin da yawan tunani ya yi wa mutane yawa, ko da tunani ne akan abinda basu da ikon canzawa. Yawan tunani bashi da wani fa'ida sai dai ya haifar wa mutum da yanayi na rashin natsuwa da kwanciyar hankali. Hasali ma yanzu cutar damuwa (DEPRESSION) ya yawaita, kuma cikin musabbabin akwai keɓe kai cikin tunani.
Allah ya ƙara mana lafiya ya bada ikon kiyaye wa.
Daga,
Pharm. Musa A Bello naku a koda yaushe