Fiye da tiransifoma 80 aka lalata cikin kwanaki 10 sakamakon rashin Lantarki — JED

Fiye da tiransifoma 80 aka lalata cikin kwanaki 10 sakamakon rashin Lantarki —  JED

tiransifoma


Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Jos (JED) ya bayyana cewa sama da taransifoma 80 ne aka lalata da kuma sace wayoyin cikinta a lokacin da aka samu matsalar daukewar lantarki. 


Kamfanin ya kuma bayyana cewa, an sace manya-manyan wayoyin wutar masu samar da wutar lantarki ga unguwanni a tsawon lokacin, inda ya ƙara da cewa jihar Filato ta fi shafar matsalar.


Shafin Aminiya ya rawaito cewa, Babban jami’in fasaha mai kula da ayyuka, Injiniya Hamisu Wakili Jigawa ya bayyana hakan a hedikwatar kamfanin JED a ranar Juma’a.


A cewar jami’in fasaha, ayyukan masu lalata tiransifoma ɗin sun kawo naƙasu wajen samar da wutar lantarki cikin sauƙi da inganci ga unguwannin da abin ya shafa.


Ya kara da cewar “ɓarnar da aka yi wa na’urar tiransifoma ɗin wajen satar wayoyin wutar sun kawo ƙalubale sosai. Matsayin ɓarnar ta yi yawa. Wasu layukan sun riga sun lalace gaba ɗaya.


“ Wayoyin na’urorin al’miniyom ɗin da ke rabar da wutar ga wasu unguwannin gaba ɗaya sun lalace. Muna da kusan ƙarfin wuta 213 kɓs waɗanda gaba ɗaya ba su da na’urori na rabar da wutar kwanaki.


 A jiya ne muka iya gyara na ƙarshe. Mun yi asarar na’urorin rarraba wutar da yawa musamman wayoyin da suke rarraba wutar lantarki daga tiransifoma.


A wasu lokuta, masu ɓarnar suna buɗe tiransfoma, su kwashe mai a ciki da komai gaba ɗaya. Tankin ya zama fanko kawai, “in ji shi.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post