Duk Yadda Kike Son Mijinki Kada Ki Bari Ya Saba Miki Da Wadannan Abubuwan |
Hankali da kyawawan dabi'u ke yiwa mai yinsu tasiri. Don haka muddin ka hango na kusa da kai yana bijirowa da wasu halayen da zai illatashi nan gaba. Yi kokarin dawo da shi kan hanya.
Mata suna yin sakaci zurawa mazajensu idanuwa bayan sun yi aure su cigaba da aikata wasu halayen da suke kuntatawa mace amma kuma babu yadda zata yi saboda tun a farko bata takawa abun burki ba.
Ga wasu halaye da dabi'un maza da duk yadda kike son mijinki, kada ki bari ya ci gaba da yinsu.
1: Kada ki sake ki bar mijinki ya saba da kasala. Wasu mazan basu da lissafi, kullum suna gida daga ci sai bacci har sai abunda suka tanada ya kare kamin su fita neman wani. Wannan ba hali bane da mace zata bari har mijinta ya saba da shi. Ganin yadda namiji yake da nauyin iyalansa, dole ne ya zama mai kazar kazar ne ba mai kasala ba.
2: Duk yadda kike son mijinki kada ki bari ya raina iyayenki ko 'yan uwanki. Akwai wasu mazan da kirikiri suke ambatar sunan iyayen matansu su dura musu zagi. Ko kuma suyi wata bakar maganar da zasu jinginata ga iyayen matansu ko 'yan uwansa. Don haka tun farko ko a wasa kada ki bari mijinki ya raina miki iyaye.
3: Akwai mazan da suke shaye shaye. Kuma idan sun tashi yi basa kunyan matansu ko ganin girman su. Kada ki bari mijinki ya saba miki da shaye shaye. Dawowa gida a buge.
Ki tabbatar ko sigari baki baiwa mijinki fuskan ya rika Sha a gabanki idan har kinyi kokarin ya daina bai daina ba. To ki tabbatar a gidan aurenku baki bashi damar yana shaye shaye ba.
4: Kada ki sake ki zuba idanuwa kina ganin mijinki yana fita yawon dare. Akwai wasu mazan sai ma sun dawo gida sun dau wanka sunyi kwalliya su cewa matansu zasu fita hira. Duk irin yadda kike son mijinki kada ki bari ya saba miki hakan.
5: Ba zaki iya hana mijinki kara aure ba. Amma dole ne ki tabbatar kin takaita yawan mu'amalar sa da matan waje. Muddin mijinki ya maida mata sune abokan rayuwarsa ba tare da harkar kasuwanci ko aiki ne yake hadasu ba, bama shi ba har ke rainin da zasu masa zai shafeki.
Wadannan sune wasu daga cikin abunda mata zasu kiyaye wajen saisaita mazajensu.
Sai dai, hana namiji abunda ya saba yi ba sauki ne da shi ba. Ba kuma nan take abun zai samu ba. Kuma ba da tashin hankali ko rigima hakan zai samu ba.
Da fatan matan da suke fuskantar irin wannan matsalar zasu yi amfani da hakuri, dabaru wajen hana mazansu aikata abubuwan da basu da kyau.
you have try even though I'm not a woman
ReplyDelete