Cizon Kare Ya Sa Ma Ta HIV (Cuta Mai Karya Garkuwar Jiji)

Cizon Kare Ya Sa Ma Ta HIV (Cuta Mai Karya Garkuwar Jiji)

Cizon Kare Ya Sa Ma Ta HIV (Cuta Mai Karya Garkuwar Jiji) 


Biki saura sati biyu angon yazo gari daga garin da yake karatu a jami'a ajin karshe. Yazo ne domin ayi gwajin HIV tunda a da can na genotype Kawai akayi.


Suka je asibitin gwamnati aka dibi jini aka yi gwaji, da sakamako zai fito sai aka ga yarinya tana da HIV shi kuma bashi da shi. Ga ta yar shekaru sha takwas (18), fara, kyakkyawa ga siffa da halitta. Wallahi abin akwai daure kai duk da an san yarinyar nada samari da yawa.


Sai aka ce suje wani wajen a sake gwaji, suka wuce babban asibitin koyarwa na jahar, nan ma aka tabbatar da tana dashi. Sai suka je laboratory na private akayi gwaji aka tabbatar da tana dashi.


Nan ne fa maman tace daman an ce HIV daga kare aka samo shi, kuma wani kare ya cije ta kwanakin baya. Maganar rainin hankali ne Wannan.


Maganar gaskiya rashin kamun kai ya haifar ma yarinyar da wannan jarabawar, rasuwar babansu ya bata daman yawoce yawoce kuma maman bata kwaba mata. 


Abin takaici shi ne har yanzu kuma basu ainihin yarda tana dashi ba kuma bata zuwa amsar magani. Wallahi ko jiya sai da naga yarinyar nan da idanuwa na. Kyaun kowa kin wanda ya rasa. 


Yanzu duk wanda yazo zai aure ta bai ce aje ayi gwaji ba sai an cuce shi wallahi saboda maman taso a rufe lamarin tun farko a cuci wancan angon.


Shi dai angon ya fasa, har yafe musu kuɗin auren da ya kai yayi. Da aka tambaye shi mai yasa yazo musamman kawai yace ayi wannan gwajin, cewa yayi wallahi yana makaranta ana lectures abin ya fado mai a rai shi yasa yazo a yi. Nace lallai Allah na sonka.


Ha'inci ne shi ne rashin sanar da ango ko amarya game da wannan laluran kafin aure. In an sanar amma ya amince ko ta amince su dinga shan magani tare suyi auren su, wannan ba ha'inci. 


Jama'a a rika yin gwaji kafin aure. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post