Ciwon sanƙarau da zazzaɓin lassa sun kashe ƴan Nijeriya 762 a shekara ɗaya |
Cibiyar Kula da Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) ta baiyana cewa mutane 762 a fadin Nijeriya ne su ka mutu sakamakon cutar sankarau da zazzabin Lassa tsakanin 2023 zuwa 2024.
Babban daraktan hukumar, Dr Jide Idris ne ya bayyana haka a jiya Talata a Abuja, yayin da yake bayar da karin haske kan cutar zazzabin Lassa da kuma barkewar cutar sankarau a kasar.
Idris ya ce mutane 361 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar sankarau a fadin kananan hukumomi 174 a cikin jihohi 23 da kuma babban birnin tarayya Abuja yayin da zazzabin Lassa ya yi sanadiyar mutuwar mutane 401 a jihohi 28.
Ya kuma ce an gwada mutane 4,915 da ake zargin sun kamu da cutar sankarau, yayin da 380 aka tabbatar sun kamu da cutar a cikin lokaci guda.