Cikakken bayani kan istimna’i

Cikakken bayani kan istimna’i (masturbation)
Cikakken bayani kan istimna’i (masturbation)


Mutane dayawa sun turo min sako cewa wallahi suna fama da wannan matsalar saboda haka suna neman mafita


Daga cikinsu akwai wani yaro mai shekaru 18 dan makaranta, yake gayamin cewa wallahi doctor abunnan yashiga rayuwata kullum cikin aikata shi nake.


Maganar gaskiya shine:

Mafi yawan matasa da yan mata suna aikata wannan dabi’ar, daga cikin mutane kadan ne zaka samu basayi.


Ba wani maganin bature ko maganin gargajiya dake warkar da wannan dabi’ar, idan ma kana neman maganin masturbation to kasani cewa kana batawa kanka lokaci ne a banza.


Menene Istimna'i (masturbation)?

Masturbation (istimna’i) yana nufin biyama kai bukata, zakaga maza suna amfani da hannunsu suna shafar azzakarinsu har maniyi ya fito musu. Mata kuwa sukanyi amfani da yatsa ko azzakarin roba, ko carrot ko cucumber domin biyama kansu bukata.


Matakin Istimna'i (masturbation):


1. Akwai wanda yanayin wannan dabi’ar so daya acikin sati.

2. Akwai wanda duk bayan kwana biyu zayyi masturbation.

3. Akwai wanda duk safiya ne zayyi masturbation.

4. Akwai wanda so biyu yake masturbation a rana.


Illolin Istimna'i (Masturbation):


1. Maganar gaskiya masturbation bayada wata illa acikin lafiyar dan adam, baya kawo rashin ganin ido, baya kawo ciwon kansa, baya kawo saurin tsufa da sauransu kamar yanda mutane ke fada duk ba gaskiya bane.


2. Yin masturbation a kullum ko so biyu a rana, zai sa kazamo masturbation addict. Idan kuwa yazame ma addicted, babbar matsala ce dake haifar da (Bakin ciki da bacin rai, rashin son zama cikin mutane, saurin fushi, da sauran psychological disorders).


3. Duk mai masturbation yanada wahala ya iya tsayar da sallah, duk wanda sallah ke masa wahala to tabbas sauran ibadodi babusu-babu labarinsu.


4. Duk mai masturbation, idan kai namiji ne zaka iya kaiwa wani mataki da baka sha’awar mace, bakajin dadi jima’i da mace.


Idan ke mace ce zaki iya kaiwa wani mataki da bakya sha’awar namiji. Zakaga mace takai shekaru 30-35 batada miji kuma ba damuwa a zuciyarta. 


Menene Mafita??

1. Wanda yake yin masturbation ko so biyu a rana, shawara mafi amfani agareshi shine yayi aure.


2.wanda yakeyin masturbation bayan kwana biyu, shawara mafi amfani agareshi shine ya rike yin azumin Litinin da Alhamis. Domin kuwa azumi yana rage sha’awar yin jima’i a jikin dan adam.


3. Wanda yakeyin masturbation so daya acikin sati, wannan zai iya barinsa nan take domin kuwa bai kai wani mataki mai hatsari ba.


Shawara:

Yanada wahala mutum yabar masturbation a rana daya, amma akwai hanyoyin da zakabi domin rage yin wannan dabi’ar kamar haka:


1. Kar ka zauna kai kadai baka tare da kowa. Kaje cikin abokaninka, ayi wasa da dariya, aje yawo, matukar ka zauna baka tare da mutane to zaka shiga tunani da zai jefaka acikin wannan yanayin.


Idan kai dan kasuwa ne ka zama busy a wurin harkokin kasuwancinka


Idan kai dan boko ne, kazama busy da karatunka kodayaushe kana karatu, kana library, kana masallaci.


2. Idan kana a cikin gida ko a dakinka, ko yaushe kabar kofofin dakin a bude, da windows 


3. Barin kallon videos ko photos na batsa.


4. Barin sex chat da yan mata, ko kiran wayar yan mata. Idan ke mace ce banda sex chat da samari ko kiran wayar samari video call.


5. Idan kai musulmi ne to kayi kokari ka tsayarda sallah acikin jam’i na kwana 40 batare da kayi missing ba. 


Tabbas idan kayi haka, dakai da masturbation kunyi hannun riga.


Idan kanada tambaya rubuta a comment.


Dr. Alhassan Mai Lafia

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post