Bukatuwar Dalar Amurka A Kasuwar Canji Ya Jawo Naira Ta Kara Faduwa |
Sakamakon Yawan Bukatar Dalar Amurka Da Ake Yi A Kasuwar Canji, Naira Ta Kara Karyewa.
Naira ta fadi a kasuwar bayan fage, ana canji da ita kan N1,750/$.
Naira ta fuskanci karin karaya a kasuwannin da ba na hukuma ba sakamakon yawan bukatar dala da kuma tabarbarewar kayayyaki.
Farashin kudin Najeriya ya yi kasa, yayin da da dalar Amurka takai N1750 a tsakiyar mako a kasuwar bayan fage na babban birnin kasuwancin kasarnan, sakamakon tsananin bukatar kudin waje da ake.
Bayanai daga dandalin ciniki na FMDQ Exchange na nuna cewa darajar Naira ta ragu da N11.4/, daga N1,690/$ da ake ciniki a ranar Litinin, zuwa N1750/$.