Bikin ƴar Kwankwaso da dan gidan Dahiru Mangal -- Fadar gwamnatin Kano

Bikin ƴar Kwankwaso da dan gidan Dahiru Mangal -- Fadar gwamnatin Kano
Bikin ƴar Kwankwaso da dan gidan Dahiru Mangal -- Fadar gwamnatin Kano 


Bikin ƴar Kwankwaso da ɗan Mangal: Gwamna Abba Gida-Gida ne zai ba da amaryar zuwa ga angon 


Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf zai ba Dr. Aisha Rabi'u Musa Kwankwaso, aure ga Engr. Fahad Dahiru Mangal a ranar Asabar mai zuwa.


Dr. Aisha, ita ce 'yar Auta ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar NNPP a 2023, kuma za ta angwance da Engr. Fahad, ɗan fitaccen attajirin kasuwanci na jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal.


A wata sanarwa daga mai magana da yawun gwamnan, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa, a ranar Talata, an bayyana cewa za a gudanar da daurin auren a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2024, wanda zai ja hankalin manyan mutane a cikin al'umma.


A cewar Malam Dawakin Tofa, iyalan biyu suna farin cikin gayyatar abokai, iyalai, 'yan siyasa, 'yan kasuwa, shugabannin masana'antu, shugabannin addini da na gargajiya domin halartar taron da za a gudanar a fadar Sarki, Kofar Kudu, a Kano.


Sanarwar daga Sanusi Bature ta bayyana cewa ana sa ran manyan baki daga ciki da wajen ƙasa domin halartar wannan biki, saboda haka an umurci jami'an tsaro su tabbatar da ingantaccen tsaro da kuma sauƙaƙe zirga-zirgar ababen hawa tsakanin gidan gwamnati da fadar sarki.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post