Ban yi laifin komai ba Tinubu ya cire ni - Tsohon Minista, T. Gwarzo

Ban yi laifin komai ba Tinubu ya cire ni - Tsohon Minista, T. Gwarzo
Abdullahi Tijjani Gwarzo


Tsohon ƙaramin ministan gidaje na Najeriya, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya ce ya yi mamakin sauke shi da a aka yi daga muƙaminsa.


Yayin wata hira da BBC kwanaki bayan sauke shi, T Gwarzo ya ce babu wani laifi da ya yi, wanda ya janyo aka sauke shi daga muƙamin nasa, saboda a cewarsa ya yi iya baƙin ƙoƙarinsa a muƙamin da aka ba shi.


''Batun ya zo min da mamaki, domin ba na tunanin wani abu mai kama da wannan zai faru da ni'', in ji shi.


Ya ƙara da cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi la'akari da tarayyarsu tun ta da can wajen naɗa shi muƙamin.


Ya ce fiye da shekara 14 suna tare da Tinubu tun a jam'iyyar ACN, shi da Nuhu Ribadu da Sanata George Akuwam - da ke riƙe da muƙamin sakataren gwamnati a yanzu.


Sai dai ya ce Allah ne ke ba da mulki, kuma ya karɓe a duk lokacin da ya so, don haka ya ce yana gode wa shugaban ƙasar, bisa damar da ya ba shi a gwamnatin tasa.


Rahoto Daga Shafin, Daily Nigerian


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post