Kanuri |
Kanuri, suna ne na wata ƙabila daga cikin manyan ƙabilun Arewacin Najeriya, waɗanda suka taɓa kafa ɗaya daga cikin dauloli guda biyu mafiya girma a duk faɗin Afirka ta yau.
Mutane ne da suka samo asali daga ƙasar Yemen. Su na da matuƙar riƙo da al’adunsu na gargajiya, da addini, da ƙarɓan baƙi da kuma uwa-uba hidimtawa Al-Kur’ani da masu hulɗa da shi da suka shafi koyo, koyarwa, hadda, rubutawa da kuma masu karanta shi.
Babban birnin su; Watau, Maiduguri, a na yi masa kallon matsuguni ko kuma masaukin mahaddata da kuma makaranta Al-Kur’ani.
Al'adunsu Na Aure
Haƙiƙa Kanurai su na ɗaya daga cikin ƙabilu da suka fi kowace ƙabila iya riƙon aure da gudanar da al’adu a yayin aure.
Kanuri |
Al’adun nasu sun haɗa da;
° Bawaram
° Fafurai
° Wushe-Wushe
° Klatul
° Kalawa
° Ka’aji
° Humram
° Kalaicam
° Kalam-Wuri
° Kndai
° Kususuram
° Wushe-Wushen Yaa’ye
° Nalle
° Tulur
° Ksai lewa
° Kaulu
° Ganga-Kura
1 - Bawaram: Kalmar Bawaram ta na nufin babanni. Idan kuwa a aure ne aka ce Bawaram, to ana nufin kayayyakin da Ango ya ke yi wa dangin Amarya, waɗanda suka haɗa da;
° Ya - Uwa
° kamu ba’aye- matar uba ko matan uba
3 - Bawa- Ƙannen uba da yayun shi
4 - Yakura - babbar yayar amarya
5 - Am ngawoye- mutanen baya
6 - Duhuram - mai kitso
7 - Ka’aram - kakanni
8 - Ya njimma- uwar ɗaki.
2 - Fafurai: Fafurai wani akwati ne da gidan amarya suke yi wa ango.
Alaadun Kanuri |
Abubuwan da ake sakawa a cikin akwatin sun haɗa da, shaddodi, yadiddika, huluna, sallaya, turare, agogo, takalma da sauran su.
3 - Wushe- wushe: Biki ne da ake gudanarwa tsakanin ɓangaren amarya da na ango, ana gobe ɗaurin aure.
Ɓangarorin biyu sukan yi shigar al’ada irin ta Kanurai su haɗu a wata farfajiya ko kuma su kama fili domin yin wannan bikin.
4 - Qlatul: Qlatul ya na nufin wanke kai, mata kaɗai ake yi wa. Ana yin sa ne idan aure ya saura kwana uku.
Yadda ake yin sa shi ne, babannin amarya ne suke wanke kan amarya da ruwan Karkashi. Bayan an kammala wanke kan, ana yin kiɗan ƙwarya; wadda tsofaffin mata suke waƙe cikin harshen Kanuri.
5 - Kalawa: Tamkar shaɗi ya ke, saidai shi ba bugu ake yi ba. Yadda ake yin sa shi ne, ana tanadar Akushi da busasshen Karkashi da farar shinkafa, sai azo da ango ko amarya a ɗora bisa wannan shinfiɗar, daman an ɗora tuwon buski ko shinkafa bisa wuta.
Ana sauke wa za a ɗebo shi da zafinsa, sai ango ko amarya su buɗe tafin hannunsu a zuba musu a kai da zafinsa, sai su kuma (ango ko amarya) su juye abincin da aka zuba masu a tafin hannu a cikin wannan akushin.
Yar kabilar Kanuri |
Anayin hakan har sau uku, sannan sai a goge masu hannayensu, a shafa masu busasshen karkashin.
Daga nan sai ƴan uwa da abokan arziki su zo su yi masu kyaututtukan alfarma. Ma’anar yin wannan al’adar shi ne, yadda suka riƙe wannan abincin da zafinsa, Allah ya sa su riƙe wannan auren fiye da haka.
6 - Ka’aji: Ya na nufin turaren wuta. Ango ne ya ke bayar da kuɗin sayen turaren wuta wadda amarya take zuwa da shi ɗakinta, wannan ma ya na ɗaya daga cikin al’adar Kanuri wadda wasu ƙabilu suka ara a yau.
7 - Humram: wani nau’in turare ne na ruwa wadda mata suke shafawa a jikinsu. Shi ma ango ne ya ke bayar da kuɗin sayen sa.
8 - Kulaicam: Shi ma nau’in Humram ne, sai dai shi da man shafawa ake haɗawa a shafe jiki. Shi ma ango ne yake bayar da kuɗin sayen sa.
9 - Kalan-wuri: wuri kuɗi ne na da da ake amfani da shi, kalan- wuri wani abu ne ƙarami kamar kafbasa wadda ake manne shi da kuɗi gaba ɗayansa a bai wa amarya ta tafi da shi ɗakin mijinta a matsayin kyauta.
Duk lokacin da buƙatar kuɗi ya same ta kuma babu kuɗin a hannunta, sai ta ɗaye wannan kuɗin da ke liƙe ta yi uzurinta da shi.
Ita wannan al’adar, takwarar amarya ce take yi mata, idan kuma bata nan (ta mutu) sai yayarta ko ƴan uwanta su yi.
10 - Kndal: kalmar Kndal asalinta ta Kanurai ce, Kndal wani ɗan kwano ne ko kuma Akushi da ake saƙa shi da kaba, da Hausa sunansa (adudu) ana yi masa ado, sai a zuba goro da fure ko Dabino a ciki amarya ita take zuwa da shi gidanta.
Idan mijin mai cin goro ne, sai ya yi amfani da shi; Idan kuma ba ya ci ita ma ba ta ci; Sai ta dinga sa Dabino ko wani abu da take buƙatar ajiye wa a ciki.
11 - Kususurum: Abin da ake nufi da Kususurum shi ne, kai kayan lefe, yadda ake kai kayan lefe a al’adar Kanurai ya bambanta da na sauran ƙabilu.
Idan za a kai kayan lefe gidan iyayen amarya a al’adar Kanurai, ana haɗawa da tinkiya, bijimi ko saniya.
Za a ɗaura atamfa a wuyan tinkiyar ko bijimi ko Saniya a yayin da za a kai kayan lefen. Wannan atamfar da aka ɗaura a wuyan dabbar, idan aka je gidan iyayen amarya, su na ba da ita kyauta ga wadda ko waɗanda suka riƙo dabbar a yayin kai kayan lefen.
12 - Wushe-wushen yaa’ye: Anayin sa ne a ranar Alhamis. Yadda ake yin sa shi ne, dangin amarya ne za su haɗu su yi nakiya, a yayin da ɓangaren ango kuma za su kawo masu goro tare da yi masu sannu da aiki; sai ɓangaren amarya su ba su wannan nakiyar da suka yi.
13 - Nalle: Ya na nufin lalle ko sa lalle, ana yin sa a ranar Talata. Ɓangaren ango za su kai buhun lalle da cingam ko minti har ma da goro da dai sauransu zuwa gidan iyayen amarya.
14 - Tulur: Kalmar Tulur a Kanuri ya na nufin bakwai. Shi tulur a auren Kanurai kuma, ya na nufin zaman bakwai da mace ɗaya ko biyu suke yi a gidan amarya na tsawon kwanaki bakwai.
A wannan zaman, waɗannan matan su za su riƙa yi ma amarya girki da shara da wanke-wanke da dai sauran hididdimun cikin gida har na tsawon wannan kwanaki bakwai.
Bayan kwanakin sun cika, ango ya na yi wa waɗannan matan kyautar atamfa da sabulai da turare, wani ma har da kuɗaɗe.
15 - Ksai lewa: Gaisuwar iyaye, ana yin sa ne a washegarin ɗaurin aure, idan ango da abokanansa za su kai ziyaran gaisuwa zuwa wajen iyayen amarya.
16 - Kaulu: Ango kaɗai ake yi wa; Yadda ake yin sa shi ne, ana dama Karkashi ne da ruwa, sai mahaifin ango ko ƙanin mahaifinsa, kai wani lokacin ma maigidansa na wajen aiki ko sana’a ne zai shafe masa hannunsa da wannan ruwan Karkashin.
Wannan fata ne na duk abin da ya mallaka ya yauƙe wato ya yi (albarka).
17 - Ganga - Kura: Kiɗan gargajiya ne da ake yin sa ranar ɗaurin aure. Dangin amarya ne da na ango maza da mata za su haɗu su yi shiga irin ta al’ada su fito su rausaya a tsakanin juna.
AL’ADAR WUSHE- WUSHE
Al’adar Wushe-Wushe ɗaya daga cikin manyan al’adun Kanuri ce wadda suke gudanarwa a lokacin bikin aure, kalmar wushe- wushe ta na nufin (sannu-sannu) ko (sannu da zuwa - sannu da zuwa) a harshen Hausa, ana yi wa dangin ango sannu da zuwa ke nan.
Al’ada ce wadda Kanuri da Shuwa Arab kaɗai ke yin ta, kuma al’ada ce mafi girma a wurin ƙabilar Kanuri da ke jihar Borno.
Bikin Wushe-Wushe dai ana ɗaukarsa a matsayin al’amari mafi ban sha’awa a dukkan bikin auren Kanuri da ke Borno a gabashin Najeriya, wadda ake yi washegarin daren ɗaurin auren.
A kan sanya waƙoƙin Sudan, da Alita, sannan a kan busa ƙaho, da buruji, da sarewa, tare da doka ganguna, duk domin wannan shagali.
Ɓangaren amarya ne ke yin wannan al’adar a washegarin ranar ɗaurin aure. An fi gudanar da wannan al’adar a ranar juma’a; Kasancewar Kanuri sun fi yin aure a ranar asabar.
Amarya da ƙawayenta sukan sanya kaya irin na al’ada masu suna (ganaa kaawowa ko dangasho) amma a yanzu ba a cika samun su ba shi ya sa ake sanya lafaya.
A kan kama fili ko gida domin gudanar da wannan al’adar, amarya na saka gaana kaawowa ko dangasho, sannan takan yi ado da sarƙa da awarwaro har da sarƙan ƙafa masu tsadar gaske, kuma a kan ɗaura mata jan ƙyalle a goshi; Haka shi ma ango a kan ɗaura masa jan ƙyalle a hular sa.
Bayan gama shirye-shirye dangin ango kan zo da abubuwa da yawa su ba ma dangin amarya tare da masu sannu da aiki, ango kan riƙa takobi a hannunsa.
Bayan fili ya cika da dangin amarya da ango, a kan yi raye-raye a yi nishaɗi.
Waɗannan al’adun su na daga cikin jigon da ya sa Kanurai suka fi ƙabilu da dama juriya wajan riƙon aure.
Sai dai kuma a wani ɓangare, wasu na ganin waɗannan al’adun su na daga cikin abin da ya sa auren Kanurai ya ke da tsada, duk da cewa ba dukkan kanurai ba ne suke gudanar da waɗannan al’adun ba a yau, saboda halin yau da kullum.